Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Alhamis

11 Nuwamba 2021

15:48:25
1197663

Amurka Ba Ta Ji Dadin Ziyarar Ministan Harkokin Wajen UAE A Siriya

Amurka ta ce ba ta goyan bayan yunkurin hadadiyar Daular Larabawa na karfafa alakarta da Siriya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Wannan dai ya biyo bayan ziyarar da ministan harkokin wajen HD Larabawar ya kai a birnin Damascos na Siriya.

Da yake sanar da hakan kakakin gwamnatin fadar White Houte, Ned Price, ya ce ziyarar ta Sheikh Abdallah ben Zayed, wani lamari ne da zai kara karfafa Bashar Al’Assad guiwa, alhali ba’a kai ga samun mafita ba ta warware rikicin kasar ta Siriya.

A ranar talata ne ministan harkokin wajen Hadaddiyar Daular Larabawar, ya kai wata ziyarar aiki, a birnin Damascos na kasar Siriya, wacce ita ce irinta ta farko a cikin shekaru goma a Siriya.

Yayin ziyarar Sheikh Abdallah ben Zayed, ya gana da shugaba Bashar Al Assad da wasu manyan jami’an kasar ta Siriya.

Bangarorin sun tattauna kan batutuwa da dama da suka shafi kasashen biyu, da kuma yadda zasu karfafa alakarsu ta bangarori da dama, a cewar kamfanin dilancin labaren Siriya na Sana.

Hadaddiyar Daular Larabawa, ta yanke alakarta da Siriya ne a watan Fabarairu na 2012, bayan boren da ya rikide zuwa na neman sauyin gwamnati a Siriya wanda ya jefa kasar cikin yaki.

342/