Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : HausaTv
Litinin

8 Nuwamba 2021

12:11:01
1196738

​Musulmin Amurka Suna Bayar Da Taimako Fiye Da Kowane Dan Kasa - Bincike

Wani sabon bincike ya nuna cewa musulmi a Amurka a shekarar 2020 sun kashe kudi fiye da kowane Ba'amurke a kasar wajen taimakon marasa galihu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar Euronews ta bayar da rahoton cewa, duk da cewa musulmi ne kashi 1.1% na al’ummar Amurka, kuma matsakaicin kudin shiga na kowane mutum a tsakanin su ya yi kasa da wadanda ba musulmi ba a kasar, amma bisa ga wani rahoto da fitar a cikin wannan shekara ta 2021, taimakon kudi da suke bayarwa ya kai kashi 1.4% na tallafin da daidaikun mutane suke bayarwa domin taimakon marasa galihu.

Musulman Amurka ƴan tsiraru ne a kasar, amma kuma adadinsu yana karuwa cikin sauri fiye da kowadanne mabiya addinai, wanda bisa alkalumman kididdigar da aka yi a karkashin wannan rahoto, suna ba da gudummawar kusan dalar Amurka biliyan 4.3 a cikin shekara ga lamurra na taimako.

An gudanar da binciken ne tare da hadin gwiwar kungiyar agaji ta Islamic Relief Organisation ta Amurka, kungiya mai zaman kanta dake kare hakkokin musulmi. Fiye da Amurkawa 2,000 ne suka shiga cikin binciken a cikin watan Maris da Afrilu na 2021.

Musulman Amurka suna ba da gudummawa a matsakaicin kudi dala 3,200 idan aka kwatanta da $ 1,905 da waɗanda ba musulmi ba suke bayarwa, kuma kusan kashi 8.5% na gudummawar musulmin Amurka suna tallafawa lamurra ne da suka shafi 'yan adamtaka, ba tare da yin la'akari da bambanci addini ko akida na wadanda suke taimakama wa ba, wanda hakan ya yi tasiri matuka wajen dakushe kaifin nuna kyamar musulmi da wasu suke yi a tsakanin al'ummomin Amurka.

Fiye da kashi 84 cikin 100 na duk gudunmawar da musulmi ke bayarwa na zuwa kasar ne, sabanin ra’ayin da ake yi na cewa, musulmi Amurkawa galibin taimakonsu yana tafiya ne wajen tallafa wa wasu shirye-shirye a kasashen ketare.

342/