Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Laraba

3 Nuwamba 2021

15:31:09
1195100

Amurka Ta Dakatar Da Habasha, Mali Da Guinea Daga Tsarin Kasuwancinta

Shugaban Amurka Joe Biden, ya sanar da dakatar da kasashen Habasha, da Mali da kuma Guinea, daga samun manyan falalolin tsarin kasuwancin nan na tsakanin kasarsa da Afrika na AGOA a takaice.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Mista Biden, ya ce daga ranar 1 ga watan Janairun 2022, za’a soke kasashen uku na Afrika daga tsarin.

A wata wasika da aka aike wa majalisar Amurkar, an ce an dakatar da baiwa Habasha tallafin ne saboda take hakkin dan adam a yakin da take da masu fafatukar a ware na yankin Tigray.

Mali da Guinea ko matakin ya shafe su ne saboda juyin mulkin da sojoji sukayi.

Shi dai tsarin kasuwacin na AGOA, ya tanadi rage wasu kudaden haraji kan kayayakin da ake shiga dasu AMurka da kuma baiwa kasashen na Afrika wata falala game da kasuwancinsu musamman kan harkar biyan kudin Kwaston da kasar ta Amurka kamar yadda aka cimma a shekarar 2020.

342/