Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Talata

2 Nuwamba 2021

14:47:14
1194741

Labarai Cikin Hotuna /Ganawar Babban Sakatare Janar Na Majalisar Ahlul-Bait (AS) Ta Duniya Tare Da Wakilin Kungiyar Amal A Birnin Tyre "Suur"

Kamfanin dillancin labaran na Ahlulbaiti (AS) - ABNA - ya habarta cewa, Ayatullah Reza Ramezani, babban sakataren majalisar Ahlul-baiti na duniya (AS ) ya gana da Sheikh Hassan Abdullah, wakilin kungiyar Amal a birnin Tyre' a ziyarar da ya kai Lebanon. A wannan taro babban magatakardar majalisar Ahlul Baiti na duniya (AS) a wannan ganawa ya anbaci Allamah "Sharaful Din" da Imam Musa Sadr da cewa: sune jagorori na gwagwarmaya masu rike da tutar hadin kai sannan yace: halartar Imam Musa Sadr cikin taron da aka gudanar cikin Coci ya share fagen tattaunawa tsakanin addinai. Wakilin kungiyar Amal ya kuma bayyana fatan kungiyar ta Amal da mambobinta na cewa za su anfana da shawarwarin Shugaban Majalisar Ahlul Bait As ta Duniya ya bayar garesu.