Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

31 Oktoba 2021

14:33:41
1194006

​Amurka Na Mara Baya Ga Isra’ila Wajen Gina Matsugunnan Yahudawa A Yammacin Kogin Jordan

Wani jami'in Isra'ila ya ce ana ci gaba da gina matsugunan yahudawa a yammacin gabar kogin Jordan da Isra’ila ta mamaye ba tare da wani cikas daga gwamnatin Biden ba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Jaridar The Times ta Isra'ila ta nakalto wani jami'i na kusa da Firaministan Isra'ila Naftali Bennett yana cewa "Gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden ba za ta hana gina matsugunan Yahudawa a yammacin gabar kogin Jordan ba.

Haka nan kuma a cewar Gwamnatin Bennett tana sa ran gwamnatin Biden na da niyyar sake bude karamin ofishin jakadancinta a birnin Kudus.

A ranar 27 ga Oktoba, kwamitin tsare-tsare na Ma'aikatar Yakin Isra'ila ta amince da gina gidaje 3,144 da ba bisa ka'ida ba a Yammacin Gabar Kogin Jordan.

Wannan ne dai karon farko tun bayan shugabancin Joe Biden, Isra’ila ta kudiri aniyar gina matsugunna yahuadawa a cikin yankunan Falastinawa da ke gabar yamma da kogin Jordan.

Yanzu haka dai akwai matsugunan yahudawa 13 da Isra’ila ta gina ba bisa ka'ida ba a Gabashin Kudus, da kuma wasu 253 a Yammacin Kogin Jordan, inda Yahudawa sama da 660,000 suke.

A karkashin dokokin kasa da kasa, ana daukar dukkan matsugunan Yahudawa da aka gina a cikin yankunan Falasdinawa da cewa aiki ne na mamaya wanda ba ya bisa ka’ida.

342/