Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

23 Oktoba 2021

18:05:01
1191521

​Sojojin Siriya Sun Hana Tawagar Sojojin Amurka Wucewa Ta Kan Wani Titi A Hasaka

Sojojin kasar Siriya sun tilastawa wata tawagar sojojin Amurka a lardin Hasaka komawa baya bayan da suka toshe wata babban hanyar da sojojin Amurkan suka saba bi a arewa maso gabacin lardin Hasaka.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta Prestv a nan Tehran ta bayyana cewa sojojin kasar Siriya sun hana sojojin Amurkan wucewa ta kan titin da ake kira M4 Highway ne bayan korafe-korafen mutanen yankin da cewa sojojin Amurkan suna muguna masu.

Bayan da suka ga cewa ba za su sami damar wucewa ba, sojojin na Amurka sun juya sun koma daga inda suka fito.

Tun shekara ta 2014 ne sojojin Amurka da sunan yaki da kungiyar Deash wacce ta kafa don tada tarzoma a kasashen Siriya da Iraki, sun shigo kasar ba tare da amincewar gwamnatin kasar Siriya ba. Banda haka suna satar danyen man fetur da ke yankin suna fita da shi zuwa kasar Iraki sannan daga can zuwa kasashen waje.

Rahotanni sun bayyana cewa babu wani maida martanin da sojojin ba Amurka suka yi. Hakama sojojin Siriya basu yi amfani da karfi don hana su wucewa ta kan titin ba.

Banda haka ko a cikin kwanakin da suka gabata wasu mutane a lardin na Hasaka sun hana tawagar sojojin Amurka wucewa ta cikin garinsu.

342/