Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

23 Oktoba 2021

18:03:03
1191518

Amurka Ta Sanar Da Hallaka Wani Babban Jigon Al-Qaida A Siriya

Ma’aikatar tsaron Amurka ta sanar da hallaka wani babban jigon kungiyar Al-Qaida a wani harin jirgi marar matuki da ta kaddamar a Siriya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A sanarwar data fitar ranar Juma’a, Amurka, ta ce ta hallaka Abdul Hamid al-Matar, a wani hari da ta kai da jirgi marar matuki samfarin MQ-9 a yankin Soulouk arewa maso yammacin Siriya.

Saidai Amurkar ba ta bayyana ko harin na maida martani ne ba kan harin da aka kai ranar Laraba kan sansanin sojojin kawance na yaki da mayakan dake ikirari da sunan jihadi.

Amma ta ce kungiyar ta Al-Qaida na ci gaba da zama babbar barazana ga AMurka da kawayenta, inda mayakan kungiyar ke amfani da Siriya domin shiryawa da kisa hare hare a kasashen ketare.

Kuma ta ce hallaka babban jigo na Al-Qaida babban koma baya ne ga kungiyar a shirye shiryenta na kai hare hare ga Amurkawa da fararen hula wadanda basu ji basu gani ba.

Dama dai a karshen watan Satumba, Amurka ta hallaka wani shugaban kungiyar ta Al-Qaida a Siriya cewa da Salim Abou-Ahmad, a wani harin sama kusa da yankin Idleb.

342/