Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Jummaʼa

22 Oktoba 2021

16:05:12
1190989

Najeriya : An Dage Shari’ar Nnamdi Kanu, har Zuwa 10 Ga Watan Nuwamba

Babbar Kotun Najeriya da ke Abuja ta dage sauraren karar da jagoran ‘yan a waren Biafra Nnamdi Kanu, ya shigar a gabanta.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : An dai dage sauraren karar ta Kanu har sai zuwa ranar 10 ga watan Nuwamban mai zuwa.

Alkalin da ya saurari karar ya ki amincewa da bukatar da lauyoyinsa suka bukata ta a dauke shi daga hannun jami'an DSS zuwa gidan yari.

Da safiyar ranar Alhamis ne babbar Kotun Najeriyar ta fara zaman saurarar karar jagoran na masu fafutukar kafa kasar Biafra a Najeriya.

Dama dai an dage sauraren karar a cen baya.

An kai Kanu kotun cikin rakiyar jami'an tsaro wadanda suka hana 'yan jarida daukar hotonsa.

Hukumomi a Najeriya, na tsare da Nnamdi Kanu ne tun bayan tuso keyar shi daga ketare, inda suke tuhumarsa da jerin laifuka guda bakwai ciki har da na ta’addanci da cin amanar kasa da kuma cin mutuncin shugaban kasa baya ga tunzura jama'a.

342/