Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

18 Oktoba 2021

14:41:14
1189855

An Sace Amurkawa 15 A Kasar Haïti

Rahotanni daga Haiti na cewa wasu ‘yan bindiga sun yi garkuwa da mutane da dama a kasar ciki har da wasu Amurkawa 15.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Mutanen na wani rukunin ma'aikatan addinin Kirista na sa-kai, wadanda suka hada da iyalansu ciki har da yara.

Babu wani cikakken bayani game da garkuwa da mutanen amma mahukunta a Amurkar sun ce suna sane da lamarin.

Haiti na daya daga cikin kasashen da aka fi aikata garkuwa da mutane a duniya, yayin da 'yan bindiga ke amfani da rikicin siyasa da rashin tsaro don neman kudin fansa.

Wani bayanai da aka fitar sun nuna cewa sama da mutum 650 akayi garkuwa dasu domin neman kudin fansa tun daga farkon wannan shekara ta 2021, wanda ya linka har sau uku idan aka kwatanta da bara warhaka.

342/