Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Litinin

18 Oktoba 2021

14:40:28
1189854

Gwamnatin Venezuela Ta Fasa Shiga Tattaunawa Da ‘Yan Adawa Na Kasar

Gwamnatin Venezuela, ta ce ba za ta halarci tattaunawa karo ta hudu da ‘yan adawa na kasar wacce aka shirya yi a Columbia ranar Litini 18 ga wata Oktoban nan.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Gwamnatin ta ce ta yi hakan ne saboda mika wa Amurkla wani dan Columbia makusancin shugaba Nicolas Maduro, wanda Amurka ta ce tana nema bisa zargin halata kudaden haramu.

A ranar Asabar ne, aka tisa keyar Alex Saab, zuwa Amurka daga Kasar Cap-Vert.

Shugaban majalisar dokokin Venezuela, ya danganta lamarin da tsokana, yayin da shi kuwa Alex Saab, ya danganta mika shin ga Amurka a matsayin haramtacce, saboda ba’a kammala shirin ba gabadaya.

Ma’aikatar shari’ar Amurka ta tabbatar da mika mata shi, kuma ta ce a ranar Litini ake sa ran za’a gabatar da shi a gaban kotun Florida.

A shekarar 2019 ne Amurka ta zarge shi da hallata kudaden haramu, da kuma kasancewa jagoran wani gungu da ya taimaka wa shugaba Venezuela, da gwamnatinsa karkata tallafin jin kai da aka baiwa al’umma Venezuela.

342/