Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

17 Oktoba 2021

15:07:10
1189437

​MDD: Mutane Kimani Miliyon 41 Ne Suke Fuskantar Barazanar Karancin Abinci A Duniya

Babban sakaren MDD Antonio Guterrez érrez ya bayyana cewa mutane akalli miliyon 41 ne a duniya suke fuskantar barazanar karancin abinci nan gaba kadan a duk fadin duniya. Sannan barazana mafi muni ita ce wacce mutanen kasar Yemen suke fuskanta.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : na kasar Iran ya nakalto Antonio Guterresz yana fadar haka a shafinsa na Twitter a daren jiya Asabar. Ya kuma kara da cewa miliyoyin mutane ne fararen hula a kasar Yemen suna fuskantar barazanar fari da kuma karancin abinci wanda yake bukatar aikin gaggawa don cetonsu.

Labarin ya kara da cewa kafin haka Devid Grossly jakadan MDD na musamman a kasar Yemen ya bayyana cewa, bayan shekaru 7 da fara yaki a kasar Yemen mutane kimani miliyon 20 ne suke bukatar taimakon gaggawa a kasar. Wannan adadi shi ne kashi 2/3 na mutanen kasar.

Grossly ya ce mutane kimani miliyon 5 ne annoban fari ko karancin ruwan sama ta fadawa yankunansu, sannan akwai kananan yara kimani 400,000 a wadannan yankuna.

342/