Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

17 Oktoba 2021

15:05:23
1189435

​Gwamnatin Kasar Venezuela Ta Dakatar Da Tattaunawa Da ‘Yan Adawa

Gwamnatin kasar Venezuela ta bada sanarwan dakatar da tattaunawa tsakaninta da ‘yan adawar kasar wanda aka shirya a yau Lahadi.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : nakalto shugaban tawagar tattaunawa da ‘yan adawa ta gwamnatin kasar Venezuela Jorge Rodriguez, yana bada wannan sanarwan a jiya Asabar. Ya kuma kara da cewa gwamnatin kasar ta dauki wannan matakin ne don nuna fushinta da kama Alex Saab daya daga cikin tawagar tattaunawa da ‘yan adawa ta gwamnatin kasar a Cape Verde da kuma mika shi ga gwamnatin Amurka a jiya Asabar.

Labarin ya kara da cewa Alex Saab ya yada zango a Cape Verde ne don samun karin makamashi a cikin jirginsa, sai jami’an tsaron Cape Verde suka kama shi suka kuma mika shi ga gwamnatin kasar Amurka.

Shugaban ‘yan adawan kasar Venezuela Juan Guaido ya yi allawadai da matakin da gwamnatin kasar Venezueala ta dauka na rashin halattan taron, ya kuma sha alwashin neman hanyoyin warware matsalolin kasar ta Venezuela. Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta taba gurfanar da Alex Saab a gaban kuliya a shekara 2019 tare da zarginsa da halatta kudaden haram da kuma raba su da shugaban kasar Venezuela mai ci Nicolas Madoro.

342/