Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Jaridar Premium times ta Najeriya ta nakalto ma’aikatar sharia ta NewYork tana cewa an kama mutane 9 daga cikin su a birnin Newjessy a ranar 13 ga watan octoban da muke ciki, sannan daya kuma a jihar Texas.
Labarin ya kara da cewa yan Najeriya wadanda aka gurfanar da su a gaban kuliya a halin yanzu dangane da wannan shari'ar sun hada da Adedayo John, 32; Oluwadamilola Akinpelu, 26; Kazeem Raheem, 29; Morakinyo Gbeyide, 39; Warris Adenuga da aka Blue, 26.
Sauran sun hada da , Lateef Goloba, 27; Samsondeen Goloba, 29; Olawale Olaniyan, 41; Olawoyin Peter Olarewaju, 34 da kuma Emmanuel Oronsaye-Ajayi, 30.
342/