Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A cikin takardar koken da ya shigar a gaban kotun duniya dake birinin Hek, mai rajin kare mahalli din dan kasar Austiriya ya bukaci da a gudanar da bincike kan shugaban kasar Barazil da gwamnatinsa game da alakar da suke da shi kai tsaye da mummunan tasirin canjin yanayi da aka samu a duniya.
Har ila yau ya zo acikin takardar cewa Bolsonaro shi ke da alhakin lalata gandun daji mai fadin Mita Murabba’I 4000, da kuma karancin ruwan sama da ake samu a duk shekara, inda ya ci gaba har zuwa kashi 88 cikin dari daga lokacin da ya hau kan mulkin a shekara ta 2019. Zuwa yau.
342/