Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

10 Oktoba 2021

16:42:49
1187513

​An Zargi Kamfanin Facebook Da Nuna Kin Jinin Falastinawa

Masu rajin kare hakkin bil adama a duniya suna zargin kamfanin facebook da nuna wariya da adawa ga al'ummar Falastinu.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, bisa binciken da masu rajin kare hakkokin 'yan adam suka gudanar, sun iya gano cewa, kamfanin facebook ya share abubuwa da dama da suke da alaka da al'ummar Falastinu, da abubuwa da aka wallafa da suka shafi Quds ko zirin Gaza.

Bayan mika koke ga kamfanin kan hakan, mai magana da yawun kamfanin na facebook ya bayyana cewa, an samu kure ne wajen goge sakonni da suka shafi falastinawa, kuma ya ce za su gudanar da bincike kan hakan domin gyarawa.

Masu kare hakkin bil adama sun ce tun daga ranar 14 ga watan Satumba da kamfanin ya ce ya kafa wani kwamiti domin bincike kan hakan, har inda yau take ba a kara jin wani bayani ko kuma sakamakon binciken ba.

Tun kafin wannan lokacin dai an jima ana zargin kamfanin na facebook da nuna karkata ga manufofin yahudawa masu zaluntar al'ummar Falastinu.

342/