Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Sahartv
Jummaʼa

8 Oktoba 2021

10:24:48
1186828

Kamfanin Google Zai Zuba Jarin $ Miliyan 1,000 A Afirka

Katafaren kamfanin Google wanda ya shahara kan neman bayanai ta Intanet ya bayyana shirin zuba jarin kimanin dalar Amurka miliyan dubu a nahiyar Afirka nan da shekaru biyar masu zuwa, domin inganta hanyoyin samun intanet a nahiyar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A ciki shirin kamfanin zai saka waya ta karkashin teku domin hada nahiyar da sabbin hanyoyin sadarwa na zamani wacce za ta ratsa zuwa kasashen Turai ta karkashin tekun.

Babban jami'in kamfanin na Google, ya bayyana cewa aikin na karkashin kasa zai bi ta kasashen Afirka ta Kudu, da Namibiya gami da Najeriya.

Sannan kamfanin na Google zai samar da bashi mai saukin biya na dalar Amurka miliyan 10 ga masu kananan sana'oi a kasashen Ghana, da Kenya, da Najeriya gami da Afirka ta Kudu, domin rage radadin da aka fuskanta sakamakon annobar cutar korona da duniya ta fuskanta.

342/