Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Laraba

6 Oktoba 2021

12:52:30
1186352

Facebook Ya Nemi Afuwar Masu Bibiyarsa

Kamfanin Facebook, wanda ya mallaki shafukan sada zumunta na Whatsapp, Messenger da kuma Instgram, ya nemi afuwar masu bibiyarsa, bayan da ya samu wata gagaruwar tangarda wadda ta yi sanadiyyar katsewarsu har tsawon sa’o’I 7 a duk fadin duniya.

Sanarwar da kamfanin ya fitar a cikin daren jiya, ta ce an samu wannan matsala ce sakamakon wasu aikace-aikace da ya yi akan na’urorinsa, matsalar da ke zuwa a dai dai lokacin da majalisar dokokin Amurka ke shirin binciken kamfanin bisa zargin yi wa dimokuradiyya karen tsaye.

Wasu bayanai sun ce kamfanin na Facebook baya daukar matakan da suka dace, duk da masaniyar da ya ke da ita game da yada labaran karyar da ake yi da shi baya ga baiwa kananan yara damar cin karensu babu babbaka ba tare da daukar mataki ba.

Tun bayan katsewar shafukan na Facebook, Watsapp da kuma Instagram bayanai sun ce miliyoyin jama'a sun tsinci kansu a hali na kaduwa inda na’urar bibiya ta tsaro ta nuna yadda matsalar ta fi shafar alummomin da ke amfani da kafofin.

Mai Magana da yawun kamfanin Facebook, wato Andy Stone da ke mika sakon neman afuwar kamfanin ga miliyoyin masu bibiyarsa cikin wani sako da ya wallafa ya ce sun yi kokarin aiki tukuru wajen magance matsalar a kankanin lokaci.

342/