Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Masu binciken sun gano cewa tun a shekarun 1980, an samu adadin mutanen da suka mutu sama da 17,000 a sakamakon gallazawar da ‘yan sandan Amurka suka yi musu.
Kusan kashi 60% na Amurkawa ‘yan asalin Afrika da suka mutu sakamakon muzgunawar ‘yan sandan, ko dai ba a bayyana su ba ko kuma an yi kuskure wajen kididdige su.
Rahoton ya kara da cewa, bayanan bogi ko kuma rashin kididdige wadannan mace-macen da aka samu zai kara boye girman mummunar matsalar nuna wariyar da hukumomin tabbatar da tsaron Amurka ke aikatawa.
342/