Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

3 Oktoba 2021

14:59:46
1185470

​Daruruwan Mutane A Brazil Sun Yi Zanga-Zangar Neman Tsige Shugaban Kasar

Rahotanni da ke fitowa daga kasar Brazil sun nuna cewa: Daruruwan mutane ne suka gudanar da gagarumar zanga-zana a manyan biranen kasar don neman shugaban kasar Jair Bolsonaro ya sauka daga kan mulkin kasar, zanga-zangar da kungiyoyin masu ra’ayin ‘yan mazana jiya suka kira , kwana daya bayan gangamin nuna goyon bayan shugaban kasar da aka gudanar.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : An gudanar da zanga-zangar ne a biranen Rio de Janero da Sao poulo da kuam Bello Horizonte da dai sauran manyan biranen kasar, wanda kungiyoyi kamar Movemento Brazil da kuma Free Brazil movement wanda suka matsa lamba na ganin an tsige tsohuwar shugabar bangaren hagu wato Dilma Roussef a shekara ta 2016

Babbar kotun kolin kasar Brazil ta bada umarnin gudanar da bincike kan shugaba Bolsonaro da na hannun damansa game da zargin da ake musu na wallafa wasu bayanan karya, kuma ta bukaci shugaban ya fitar da sunayen mutane da ake zargin domin gurfanar da su a gaban kotu,

342/