Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

28 Satumba 2021

07:54:07
1183728

MDD Ta Yi Kira Da A Kawar Da Makaman Nukiliya Daga Duniya

Sakatare Janar na MDD, ya yi kira da a kawar da makaman nukiliya a duniya baki daya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Antonio Guterres, na bayyana hakan ne a jawabin da ya yi albarkacin ranar kawar da makaman nukiliya ta duniya da ta fado a jiya Lahadi.

Yana mai cewa dole ne a kawar da makaman nukiliya daga duniya, kana a bude sabon babi na tattaunawa da aminci da zaman lafiya.

A cewarsa, kawo karshen makaman nukiliya ya kasance aikin da MDD ta sa a gaba tun bayan kafuwarta.

Mista Guterres ya ce kudurin zauren majalisar na farko a 1964, ya nemi kawar da makaman nukiliya da sauran makaman kare dangi.

Ya kuma ce, duk da cewa adadin makaman nukiliya na ci gaba da raguwa cikin gomman shekarun da suka gabata, akwai tarin wasu 14,000 a fadin duniya, wadanda ke fuskantar barazana mafi muni cikin shekaru kusan 40 da suka gabata.

Ya ce yanzu lokaci ya yi na kawo karshen wannan barazana da kawar da makaman daga doron duniya domin shiga wani sabon zamani na tattaunawa da aminci da zaman lafiya tsakanin jama’a.

342/