Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Lahadi

26 Satumba 2021

14:13:55
1183330

​Canada Ta Kawo Karshen Tsare Shugaban Kamfanin Sadarwa Ta ‘Huawei’ A Musayar Fursinoni

Gwamnatin kasar Canada ta kawo karshen tsarewan da ta yiwa shugaban kataparen kamfanin sadarwa ta ‘Huawei’ na kasar Cana bayan da kasashen biyu Amurka da Cana suka yi musayarta da wasu Amurkawa wadanda Cana take tsare da su saboda aikin leken asiri.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta Presstv a na Tehran ta nakalto kafafen yada labarai da dama su na cewa shugaban kamfanin Huawei wacce Canada ta tsare na tsawon shekaru 3 bisa bukatar gwamnatin Amurka saboda tuhumar aikin leken asiri, an saketa kuma tuni ta isa kasar Cana.

Labarin ya kara da cewa Meng Wanzhou ta bar Ottawa babban birnin kasar Canada ta kuma isa kasar Cana bayan da kasar ta sallami Amurkawa biyu wadanda take tsare da su kan tuhumar leke asiri tun da dadewa.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Cana ta tabbatar da wannan labarin ta kuma kara da cewa gwamnatin kasar ta na maraba da Meng zuwa gida cana.

Kafin haka dai gwamnatin kasar Amurka ta rufe kamfanin sandarwan ta ‘Huawei’ mai kera wayoyi masu inganci na kasar Cana a Amurka. Sannan ta kakabawa kamfanin takukumai masu yawa don hanata ci gaba a duniya.

342/