Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Mista Biden, ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya gabatar a babban taron MDD, da aka fara a wannan Talata.
‘’Tare da sauren manyan kasashen duniya, (Faransa, Biritaniya, Rasha da kuma China) Amurka na aiki ta hanyar diflomatsiyya domin dawo da Iran a cikin yarjejeniyar nukiliyar ta 2015 cikin tsanaki’’, inji shugaba Biden.
Saidai ya ce Amurka tana nan kan barkarta na hana Iran mallakar makamin nukiliya.
Kafin hakan dai kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran, Saïd Khatibzadeh, wanda ke halartar taron a birnin New York, ya bayyana cewa za’a koma tattaunawar farfado da yarjejeniyar Iran a cikin makonni masu zuwa.
342/