Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Laraba

22 Satumba 2021

16:19:35
1182329

An Bude Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya Karo Na 76

An bude babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 76 a birnin New York, in da shugabannin kasahsen duniya da dama za suyi jawabi kan abubuwan dake faruwa a duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Ana sa ran taron zai maida hankali kan batutuwan da suka shafi rikice rikice, tattalin arziki, sauyin yanayi, lafiya da dai saurensu.

Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guteres, yayin bude taron ya gargadi Amurka da kuma China kan jefa duniya cikin wani sabon yanayi na tabarbarewar al’amura bayan wanda duniya ke fama dashi a yanzu inji shi.

Mista, Guterres ya kuma nuna damuwa akan juyin mulkin da ake samu a wasu kasashe da kuma tashe tashen hankula.

Taron dai na bana na samun halartar wasu shugabannin kasashen duniya maimaikon na bara da aka gudanar ta kafar bidiyo saboda bullar annobar korona.

342/