Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

18 Satumba 2021

12:24:16
1180988

​Kasahen Iran da Rasha Sun yi Korafi Ga MDD Kan Matsalolin Diplomasiya Da Suke Fuskanta A Amurka

A cikin wata wasikar hadin guiwa wanda kasshen Iran, Rasha, Cuba, Venuzuwaila, Siriya da Nikaraguwa suka aikewa babban sakataren na majalisar dinkin duniya, kasashen sun yi korafi kan cewa Amurka na yin aiki da ya rataya a wuyarta a matsayinta na wacce ke rike da hedkwatar majalisar ta duniya.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Haka zalika wakilan din din din na kasashen a majalisar dinkin duniya sun nuna rashin jin dadinsu game da yadda kasar Amurka ke ci gaba da take yarjejniyoyin da aka cimma matsaya a kai a shekara ta 1947 inda ta bukaci a mika shari’a zuwa ga kotun sasantawa domin yi wa bakin tubkar hanci.

Musamman ganin cewa mai masaukin baki hakkinta ne ta sanar da lokacin ga dukkan wakilan kasashen duniya da za su halarci zaman babban zauren majalsar dinkin duniya ko kuma aiki a majalisar.

Daga karshe kasashen guda 6 sun bayyana cewa an kafa majalisar dinkin duniya ne bisa girmamawa da mutunta ko wacce mamba dake cikinta ba tare da wani bambanci ba,, domin bai kamata ta yarda da duk wani nuna banbanci ko wariya tsakanin mambobin majalisar ba.

342/