Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Daga cikin wadanda abin ya shafa akwai Morteza Minaye Hashemi wanda shi ne ma’ajin Amurka ke zargin yana taimakawa kungiyar Hizbullah, sai kuma kamfanin kasar China Yan SU Xuan da kuma Son jing da take zargin su da taimakawa Hashemi wajen bude asusun bankin.
Sakatare harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya fadi cewa Amurka ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen sanya ido kan ayyuakansu, kuma za ta ci gaba da daukar tsauraran matakai na dakile ayyukan da suke gudanarwa, takunkuman sun hada da kwace kadarorinsu da kuma hana yin duk wata musayar kudade da su
Ita dai kungiyar Hizbullah ta dauki wannan matakin ne domin rage radadi da Al’ummar kasar suke ciki, da yake gab da tsada kasar cik, wanda kuma ya samo asali sakamakon matsalar tattalin arziki da kuma karancin makamashi da kasar take fama da su.
342/