Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Laraba

15 Satumba 2021

11:25:28
1180024

​Amurka: Kotu Ta Daure Matar Da Ta Kai Hari Kan Masallaci A Minnessota

Kotu a kasar Amurka ta daure matar da ta kai hari a masallaci a jihar Minnessota shekaru 53 a gidan kaso.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Shafin yada labarai na Mai State Line ya bayar da rahoton cewa, kotu ta daure matar da ta kai hari a wani masallaci a jihar Minnessota a shekarar 2017 , shekaru 53 a gidan kaso.

Matar mai suna Emily Claire Harry 'yar shekaru 50 da haihuwa, wadda aka fi saninta da suna Michael Harry a yanzu abyan da ta yi tiyatar sauya jinsi, an same ta laifin kai hari a masallacin Darul Farooq da ke garin Bloomington a cikin jihar Minnessota.

Bayan kwashe tsawon watanni bakawai kotu tana gudanar da bincike, daga karshe dai ta samu matar da aikata laifin da ake tuhumarta.

Lauyoyin da suke kare ta sun bukaci a sassauta hukuncin zuwa daurin shekaru 30 amma kotu taki amincewa da hakan, yayin da lauyoyin kwamitin masallacin suka bukaci a daure ta daurin rai da rai.

Musulmin da suke salla a wannan masallacin dai sun bayyana cewa, tun daga lokacin da aka kai wannan hari, har zuwa ba su yin salla da sauran ayyukan iabada a cikin natsuwa a wannan masallaci.

Matar dai ta jefa bam ne a cikin masallacin, a lokacin a da musulmi suke ciki suna gudanar da ibada, amma babu wani ya rasa ransa ko jikkata, sai wani bangaren ginin masallacin ya samu matsala.

Matar wadda a halin yanzu ta yi tiyata inda aka mayar da ita namiji, ta bukaci a yi shari’ar ne a matsayinta na mace a lokacin da ta aikata laifin, wanda ta ce ta yi hakan ne saboda bayanai na kure da ta samu a kan musulmi da kuma masallacin nasu.

342/