Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Talata

14 Satumba 2021

09:33:13
1179683

MDD Ta Bukaci A Zurfafa Hadin Gwiwa Don Magance Rashin Daidaito

Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya yi kira ga kasashern duniya, da su zurfafa hadin gwiwa, don ganin an magance matsalar kiwon lafiya dake addabar duniya da rage talauci da rashin daidaito.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Mista Guteress, ya bayyana haka ne, cikin sakon da ya gabatar ta kafar bidiyo, albarkacin ranar hadin gwiwar kasashe masu tasowa, wanda ake bikinta a duk duniya a ranar 12 ga watan Satumban.

Yana mai cewa, akwai bukatar kasashen duniya su kara yin hadin gwiwa, don ganin an magance matsalar kiwon lafiya dake damun duniya, da rage talauci, da rashin daidaito, da cimma nasarar manufofin ci gaba mai dorewa, da magance matsalar sauyin yanayi.

Ya kuma bayyana cewa, annobar Korona ta kasance kalubale mai sarkakiya dake ci gaba da addabar duniya, baya ga yadda ta yi illa ga tsarin zamantakewa, da tattalin arziki da muhalli.

342/