Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : ABNA24
Asabar

11 Satumba 2021

11:57:52
1178963

​ Amurka Na Juyayin Shekaru 20 Da Harin 11 Ga Watan Satumban 2001

Yau Asabar, Amurka na juyayin shekaru ashirin da harin 11 ga watan Satumban 2001.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A ranar Talata 11 ga Satumban 2001, ne wasu masu alaka da kungiyar al- Ka’ida su 19 suka kwace jiragen sama guda 4 tare da kai hare-haren kunar bakin wake a Amurka kan tagwayen gine gine na Cibiyar kasuwanci ta Duniya da ke birnin New York, da ma’aikatar tsaro ta Pentagon da ke Washington, yayin na fado, a birnin Pennsylvania.

Kusan mutane 3,000 suka mutu yayin harin wanda ya kasance mani muni a tarihin Amurka.

Shugaban Amurka Joe Biden, sabanin shugabanin da suka gabace shi, ya fitar da wani faifan bidiyo maimakon yin jawabi yayin bikin zagayowar ranar inda ya bukaci Amurkawa dasu hada kansu, wanda shi ne karfin kasar inji shi.

Kafin hakan dai, Mista Biden ya342/ ba da umarnin sakin wasu bayanan sirri dangane da binciken gwamnati kan harin na ranar 11 ga watan satumban 2001.

342/