Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Alhamis

9 Satumba 2021

13:06:29
1178437

​An Sake Dawo Da Sauraren Shari’ar Mutumin Da Ya Shirya Harin 11 Satumba 2001 A Amurka

An sake dawo da sauraren shari’ar Khalid Sheikh Muhammad mutumin da ake zargi da kitsa harin 11 ga watan Satumba a Amurka.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : ya nakalto daga Jaridar Quds Alarabi cewa, za a ci gaba da gudanar da shari'ar Khalid Sheikh Muhammad mutumin da ake zargi da kitsa harin 11 ga watan Satumba 2001 a Amurka, inda Amurka ta yi imanin cewa shi ne mutumin da ya shirya harin baki daya, tare da tsara yadda aka aiwatar da shi.

An kwashe tsawon shekaru dai ana ta bin kadun wannan shari'a, wadda aka yi ta jan kafa a kanta saboda dalilai na siyasa.

Zaman sauraren shari'ar da fara daga jiya 7 ga watan satumba, zai ci gaba har zuwa ranar 17 ga wannan wata, inda Khalid Sheikh Muhammad zai gurfaa, tare da Walid Muhammad saleh Mubarak, Ali Abdulaziz Ali, Ramzi Bin Shaibah, da kuma Musatafa Ahmad Adam Hausawi.

Hukumar FBI ta kasar Amurka ta sheda cewa, kusan dukkanin bayanan da ake da su na tuhumar wadannan mutanen, tabbatattun bayanai ne, domin kuwa kusan dukkanin abin da ke ciki su ne da kansu suka yi bayani, baya ga sauran abubuwa wadada suka dogara a kan bayanan sirri da kuma shedu na mutane da kuma na hotunan bidiyo da daisauransu.

342/