Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

4 Satumba 2021

08:33:15
1176419

​Shugaban Kasar Amurka Ya Bukaci A Sake Duba Takardun Binciken Da Aka Gudanar Kan Hare-Haren 11/09 Don Gano Rawar Ta Saudiya Ta Taka Cikinsu

Shugaban Amurka Joe Biden ya bukace ma’aikatar shari’ar kasar da kuma hukumomin da abin ya shafa, da su yi bitan binciken da ma’aikatar shari’ar da kuma FBI suka yi dangane da irin rawar da gwamnatin kasar Saudiya ta taka a hare-haren 11/09 na shekara ta 2001.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S} - ABNA : Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto shugaban ya na fadar haka a jiya jumma’a, ya kuma kara da cewa dangin Amurkawa kimani 3000 wadanda suka rasa rayukansu a hare-haren su na son a bayyana sakamakon binciken da aka gudanar kan hare-haren don su gano wadanda suke da hannu a cikin hare-haren don kuma karbar diyya daga wadanda suke goyon bayan yan ta’addan da suka kai hare-haren na 11/09/2001.

Kafin haka dai an bayyana cewa mutane 19 ne ‘yan kungiyar Al-Qa’ida suka shirya kuma suka kai hare-haren, sannan da dama daga cikinsu ‘yan kasar Saudiya ne.

342/