Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Asabar

28 Nuwamba 2020

08:09:15
1089990

Iran:Mohsen Fakhrizadeh Shugaban Cibiyar Bincike A Ma’aikatar Tsaron Kasar Iran Yayi Shahadi

Shugaban cibiyar bincike na ilmin kimiyyar lissafi a ma’aikatar tsoron kasar Iran Dr Mohsen Fakhrizadeh ya yi shahada a hannun yan ta’adda a wani wuri a cikin birnin Tehrana jiya Jumma.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran Farsnews na kasar Iran ya bayyana cewa wasu yan ta’adda ma’aikatan Isra’ila (HKI) ne suka kai masa hari a garin Absard a cikin birnin Tehran a jiya da yamma.

Labarin ya kara da cewa yan ta’adan sun tada boma-bomai da kuma harba bindigogi a lokacin kai harin ta’addancin.

Mohsen Fakhrizadeh ya ji raunuka masu tsakani a lokacin, bayan an kai shiasibiti likitoci sun kasa ceto ransa saboda tsananin raunuka da ya ji. Banda shi dai akwai yan ta’adda guda 4 wadanda suka kai harin da aka halaka.

Daga Karshe majiyar ma’aikatar tsaron kasar Iran ta bayyana cewa za ta nauki fansa kan wadanda suke da hannu wajen kisar wannan babban masanin.

342/