Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : hausatv
Jummaʼa

9 Oktoba 2020

14:18:44
1076762

Sayyid Nasrallah: Ya kamata Ace Dukkanin jinsin Dan’adam Ya Amfana Da Darussan Waki’ar Ashura

Babban magatakardar kungiyar Hizbullah ta Lebanon Sayyid Hassan Nasrallah wanda ya gabatar da jawabi na rabar 40 ta shahadar Imam Hussain ( a.s) ya ci gaba da cewa; Yunkurin Iman Husain yana cike da darussa da manufofi na ‘yan’adamtaka da musulunci da imani, don haka ya kamata ya kasance ta zama darussa ga dukkanin musulmi da mutane.”

ABNA24 : Sayyid Nasarallah ya kuma ce; Da akwai damar isar da sakonnin da suke kunshe a cikin wannan yankurin na Ashura ta kafafen watsa labaru na zamani.

Sayyid Nasrallah ya yi ishara da yanayin da ake ciki na cutar corona, sannan ya yi kira da a gudanar da ziyarar 40 daga cikin gidaje,mu kuma yi tawassuli da wannan shahidin akan tafarkin Allah, da kuma kakansa manzon Allah, da mahaifansa Amirul Muminin da Zahra da dan’uwansa Hassan da sauran jagororin shiriya.

Babban magatakardar kungiyar ta Hizbullah ya kuma bayyana cewa; Yunkurin Ashura yana dauke da fuskoki daban-daban na jarunta, sadaukar da kai da kuma abubuwa masu cike da tausayi.

Sayyid Nasrallah ya kara da cewa; Yin kukan da muke yi na juyayin Imam Husain, muna taya manzon Allah ( s.a.wa) kuka ne da bakin ciki.

342/