Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Abna24
Litinin

24 Faburairu 2020

16:52:31
1012952

Video:

Bidiyon Mumunan Harin Da HK,Isra’ila Ta Kai Wa Falastinawa

Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila a safiyar Lahadi sun kai wani mumunan hari kan Falastinawa inda suka yi sanadiyar mutuwar Bafalastine daya yayin da wasu hudu suka jikkata.

Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti{a.s}ABNA24-da sanyin safiyar ranar Lahadi sun kai wani hari kan Falastinwa wanda yai sanadiyar shahadar wani matashi daya a yayin da wasu hudu suka jikkata.

Kungiyar Jahadin Musulunci tayi nuni da muni harin sannan ta kuma tabbatarwa haramtacciyar kasar Isra’ila cewa ba zasu samu damar ci gaba ta’addanci akan sauran kasashen larabawa ba.

Sun kuma kara da cewa, sai sun dauki fansar jinanen shashidansu ta hanyar zafafa hare hare akan Tel Avif.

Kungiyar ta kara da cewa,duk wani harin wuce gona da iri akan yanki Gaza wanda makiya zasu kai ba zai hana kungiyoyin gwagwarmaya ci gaba da ayyukansu ba.

Fauzi Barhum kakakin kungiyar Hamas yace,harin  gangancin da sojin Isra’ila suka kai wa  Falastinawa wanda ya janyo shahadar wani matashi da kuma wulakanta gawarsa a bainar jama’a, ya shiga cikin jerin ta’addancin da suka yi wa al’ummar Falastinawa a tsawon zamani.