Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti{a.s}ABNA-kwana Arba’in da suka wuce a wata safiya sojin Amurka sun gaddamar da wani hari ta sama akan tawagar Diplomasiya kusa da filin tashin jiragen sama na Bagadaza wanda ya yi sanadin shahadar Janar Qassim Sulemani tare da Abu Mahdi Al-muhamdis shugaban sojin sai kai tare da masu rakiyarsu.
Donald Trump shugaba Amurka yan sa’oi kadan ya fito ya dauki nauyin kai wannan harin na ta’addanci inda yace: a daren jiya bisa umarni na sojin Amurka sun gaddamar da wani hari akan babban dan ta’adda na Duniya wato Qassim Sulemani kuma suka kasha shi.
Wannan Bidiyon na sama rakiyar Gawar Sulemani ce tare da Shahid Al-muhandis da wadanda suke tare da su wanda aka yi a muhimman garuruwan Iran da Iraki inda miliyoyin mutane suka halarta kuma ya zama mafi girman rakiya a tarihin Duniya: yanzu hukunci ya rage wajenka shin wannan rakiyar Gawar dan ta’addace?