Kamfanin Dillancin Labarai Na AhlulBaiti

Madogara : Abna24
Asabar

1 Faburairu 2020

11:50:49
1006862

Cibiyar Ahlul-Baiti{A.S} Ta Duniya Ta Sanar Da Sabon Wakilinta A Saliyo

Shugaban cibiyar Ahlul-Baiti ta duniya ya nada Sheikh Ahmad Tijani Sila a matsayin sabon wakilin cibiyar a kasar Saliyo. Taskar watsa labarai ta Ahlul-Baiti{a.s}-ABNA24- ta rawaito cewa anyi bikin nada sabon wakilin ne a kasar ta Saliyo, an dai wayi wannan biki ne a ranar Laraba 29 ga watan Janerun shekarar 2020, inda taron ya samu halartar manya malamai da muballigai. Shugaban cibiyar Ahlul-baiti na duniya Ayatullah Riza Ramzani ya bayar da takardar kama aikin ta hannu wanda ya wakilce shi shekh Muhammad Mu’iniyan da kuma Sayyid Zaman Hussain ina suka mika takardar nadin ga shekh Ahmad Tijani Sila.