• Shekh Dakta Ridha Zaari’i Khurmizy: Matukar Addinin Musulunci Yana Raye To Lalle Shekh Zakzaky Yana Raye

  Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - ya kawo rahoton cewa, A yau Laraba 22/12/2021 bayan sallah Azuhur An gudanar da taron tunawa da waki'ar Zaria wacce ta faru shekaru shida da suja wuce a cikin Jami'ar Ahlul Bayt International dake Tehran inda taron ya samu halartar mutane da dama daga cikin malamai da daliban Jami'ar taron ya samu halartar Babban Malamin Jami'ar Doktor Hujjatul Islam Wal Muslimeen Shekh Ridha Zari'i Khurmizy Malami mai koyarwa a tsangayar Tarihin Musulunci na Jami'ar inda ya gudanar da bayani mai ratsa jiki ga mahalarta taron Babban Malamin ya tabo janibobi da yawa na rayuwa da ayyukan Shekh Ibrahim Zakzaky da irin kokarin da yayi yake kuma cikin yi a harkar yada Addinini Musulunci da Mazhabar Ahlul Bayt As Malamin ya tabo janibin yanda wannan waki'a ta faru da kuma irin sadaukarwar da yan uwa Musulmi su kayi na bada rayuwa kansu musamman Shekh Zakzaky da mai dakinsa inda yayi bayanin irin yadda suka rasa 'ya'yansu guda shida a waki'o'u guds biyu tare da rasa mabiya da suka haura sama da dubu bisa farmaki da hukuma take kai masu ta hanyar anfani da jami'an tsaron ksa ba tare da wani dalili ba.

  cigaba ...
 • Jawabin Sayyida Suhaila game da maganar dakatar da muzaharori

  Daya daga cikin ‘ya’yan jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sayyid Ibrahim Zakzaky watau Sayyida Suhaila Ibrahim ta fitar da wani gajeren jawabi na Bidiyo inda take bayyana cewa batun kira da dakatar da muzaharori na bayan ba shi da wani asasi, kuma ba ra’ayin mahaifin ta bane.

  cigaba ...
 • Gangamin kiran a saki Malam [H] a dandalin Coply dake Amerika

  A ci gaba da gabatar da gangami da muzaharori na kira ga gwamnatin Nigeria data gaggauta sakin jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sayyid Ibrahim Zakzaky al’ummar musulmi a kasar Amerika sun gabatar da wani gangami a dandalin Coply dake Boston na kasar.

  cigaba ...
 • ​HRW Ta Bukaci A Saki ‘Yan Shi’a A Najeriya

  Kungiyar Kare Hakkin ‘yan adam ta Human Rights Watch ta bukaci jami'an tsaron Najeriya da su daina yin amfani da karfi wanda ya wuce kima wajen tarwatsa masu zanga-zanga a Najeriya musamman ma amfani da karfin bindiga.

  cigaba ...
 • 'Yan uwa mata almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky sun yi jerin gwano a Abuja

  'Yan uwa mata almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky sun yi jerin gwano a Abuja domin neman a saki Jagoransu Dandamalin 'yan uwa mata almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky sun yi jerin gwano a Abuja domin neman gwamnati ta mutunta doka ta saki jagoransu wanda a watan gobe zai cigaba shekara biyu da tsarewa ba tare da wani dalili ba. Matan sun je Ofishin ma'aikatan kare hakkin bil Adama domin su shigar da kokensu na tauye hakkin jagoransu amma jami'an basu fito sun saurare su ba, da dalilin cewa wai suna metin. Amma daga baya sun yi izni ga wasu mata biyu sun shiga sun shigar da kokensu. Duk da jami'an 'yan sanda sun zo wurin amma basu yi komai ba ga masu jerin gwanon.

  cigaba ...
 • Yan Shi’a Mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky Sun Yi Taro Domin Wafatin Manzon Allah (sawa) A Fadin Tarayyar Nijeriya

  Jiya Juma’a tayi daddai da 27 ga watan Safar a lissafin wata a Nijeriya wadda a irin wannan ranar ce Manzon Allah (SAAw) ya bar duniya zuwa ga Allah Subhanahu wa Ta’ala. Sananne tsakanin musulmi ‘yan shi’a a duk inda suke suna zama suna raya wannan rana da addu’o’I da ziyarori da karanta siran Annabi (saw) domin daukan darasi. Mabiya Sheikh Zakzaky Kaman sauran ‘yan uwansu ‘yan shi’a na duniya sun gabatar da wannan taro a wurare da dama a fadin tarayyar Nijeriya. Sheikh Adamu Tsoho Jos a lokacin da yake bayani a wajen taron garin Jos ya tattauna abubuwa masu yawa dangane da wasicin Annabi (saw), yayi bayanin abubuwan da suka faru a Hajjin bankwana da yanda Annabi ya kalifantar da Imam Ali a Ghadeer. Shehin Malamin ya tabo batun rundunar Usama wadda Manzon Allah ya kawwana ya sanya Usama ya jagoranci Sahabbai zuwa Yemen, da rashin bin Umurnin Manzon Allah na fita tare da Usama zuwa Yemen da Sahabbai suka yi. Malamin yayi bayani dangane da rashin lafiyar Annabi a karshen rayuwarsa da abubuwan da suka faru a Raziyatu Yaumil khamis inda Sahabbai suka saba umurnin Manzon Allah na bashi tawada da abin rubutu a lokacin da ya bugace su da su bashi takarda da abin rubutu domin ya rubuta masu abinda idan suka rike shi ba zasu halaka ba har abada. Shi kuma Sheikh Sanusi Abdulkadir a lokacin da yake gabatar da jawabin a taron tunawa da wafatin Annabi a garin Kano yayi bayyana cewa wannan rana ce da bakin ciki da jajantawa ‘yan uwa musulmi. Sannan yayi bayani dangane da muhimmancin rubuta wasiya inda yake cewa a mazhaban Ahlulbait wajibi ne yin wasiya, ko a fadawa amintattu ko a rubuta a ajiye, amma rubutawa ya fi muhimmanci. Malamin ya bayyana cewa wasiyyar Manzon Allah ta kasu kashi kashi ne; Akwai wadda Manzon Allah yayi a ranar Arfa, da wadda yayi a ranar Gadeer, da kuma wadda yayi a lokacin da ya kwanta rashin lafiyar ajali. Idan a koma jawabin malamin za a ji yanda yayi bayani dalla dalla dangane da wadannan wasiyoyi na Annabi kafin ya bar duniya a 27 ga Safar. Sheikh Yakubu Yahaya ya bayyana cewa sau biyu ana ba Annabi guba a lokacin da yake jawabi a wajen taron tunawa da ranar wafatin Manzon Allah a Markazin almajiran Sheikh Zakzaky dake Katsina. Yana cewa “ An ba Annabi guba har sau biyu; Na farko, wata mata Bayahudiyya ta bashi guba cikin cinyar Akuya. Na biyu kuma, wasu mutane har da manyan Sahabbai ne suka sanya ma Annabi guba a cikin magani, sun bashi yace su sha ya gani, duk da haka sai da suka sanya mashi har ta zama sanadiyyar wafatin Annabi (saw)” Ayi irin wannan taro a garuruwan da suka hada Zariya, Bauci, Sokoto, Kauran Namoda da sauransu

  cigaba ...
 • An fara taron tunawa da munasabar haihuwan Imam Ali Ar-Rida a Kano

  Yau Alhamis,3 ga watan Agusta 2017,Harkar Musulunci a Nigeriya karkashin jagorancin Sheikh Ibrahim Yakubu Zakzaky ta fara gabatar da jerin tarukan da ta shirya domin tunawa da ranar haihuwan Imam Rida a Kano,wanda Ad-Da’iral Ammah ta saba shirya a duk shekara a Hussainiyyar Baqiyyatullah Zariya kafin a rusa ta. A wannan shekarar taron an fara yinsa ne a Markaz dake Kofar Waika Kano tarayya Nigeriya,kuma za a kammala taron ranar Asabar mai zuwa. Duk shekara akan canja tutar haramin Imam Ridha (as) da wata,wadda aka cire din ana kyautar da ita ga wani daga cikin masu hidima ga AhlulBait a duniya.To,a wannan shekarar an aikowa da Sheikh Zakzaky ita wannan tutan da aka cire a matsayin kyauta da karramawa.Bayan tutan ta isa ga Sheikh Zakzaky a in da yake a tsare.Sai Sheikh yayi umurni da baiwa Malam Sanusi Abdulkadir a matsayin girmamawa saboda sadaukarwansa,sannan kuma ya shirya taro na musamman dangane da Imam Ridha,sannan a sanya tutan a Hussainiyyar Markaz dake Kofar Waika. Daga cikin abubuwan da aka gudanar yau a matsayin rana ta farko daga cikin jerin kwanaki uku na taron,bayan bude taro da addu’a da karatun Alkur’ani da karatun Ziyara,an gabatar da jawabai masu muhimmanci a wajen taron. Sheikh Adamu Tsoho Jos a matsayin babban bako mai gabatar da kasida a wannan rana ya fara jawabinsa da taya ‘yan uwa murna na zagayowar wannan rana ta haihuwan Imam Ridha wanda bisa ludufin Allah ranar haihuwarsa ya zo daidai da ranar haihuwar ‘yar uwarsa Sayyidah Ma’asumah. Shehun Malamin ya bayyana cewa “dole mu godewa Allah na samun kanmu cikin masu raya al’amarin AhlulBait.Na farko,mu godewa iyayenmu da ba a same mu ba ta hanyar da ba ta dace ba,kuma mu ba munafukai bane kaman yanda ta tabbata a riwaya. “Ya zo a hadisi daga Imam Sadiq yana cewa Allah yayi rahama ga wanda ya raya al’amuran mu.Wannan irin taro namu yana daga cikin raya al’amarin AhlulBait.” Shi kuma Sheikh Sanusi AbdulKadir a na shi jawabin bayan ya godewa Allah bisa ga wannan karramawa da Sheikh Zakzaky yayi masu ba wai don ya isa bane,ya bayyana cewa: “Tutar Haramin Imam Ridha babu wadanda suke cirota sai mutum 4 a Iran,Sayyid Khamnae da wasu ne suke ciro ta.Bayan an ciro ta ana baiwa Sayyid Khamnae ya dauki tsawon lokaci yana tawassali da ita.Sannan ya dawo da ita yace a samu wani bawan Allah a duniya wanda yake yiwa addini hidima a bashi ita. “Shine sai aka aiko ta ga jagoranmu Sayyid Zakzaky.Shima ya dauki lokaci yana tawassali da ita a inda yake tsare yanzu,sannan kuma ya aiko da ita nan Kano yace a shirya gaggarumin taro.Sayyid yace ya so a ce yana nan ya shirya taron da yafi na baya amma yanzu Dr Sanusi yayi iya kokarinsa ya ga taron anyi.” Taron ya samu halartan ‘yan uwa maza da mata daga wurare daban daban cikin Nigeriya.Kuma taron yana gudana cikin nasara da taimakon Allah.

  cigaba ...
 • Babban taron tunawa da haihuwar Imam Ridha[AS] na shekara shekara a Kano

  Ana gayyatar daukakin al'ummar musulmi zuwa babban taron tunawa da haihuwar limami na takwas cikin jerin limaman shiriya na gidan Manzon Allah[SAWA] watau Imam Ali Ibn Musa Arridha[AS] wanda Harkar Musulunci ta saba gabatarwa a ko wacce shekara. A wannan karon za'a gabatar da wannan babban taro ne a Kano......................, Malam Sunusi Abdulkadir shine mai masaukin baki. Da yardan Allah za'a kwashe tsawon kwanaki uku ne ana gabtar da taron inda za'a soma shi tun daga ranar Alhamis zuwa ranar Asabar in Allah ya yarda

  cigaba ...
 • An yi taron tunawa da ranar Kudus ta duniya da kuma kaddamar da littafi a Abuja

  A yau Asabar,29 ga watan Yuli 2017,’yan harkar Musulunci a Nigeriya suka shirya taro na musamman domin tunawa da ranar Kudus ta duniya da kuma kaddamar da littafi a Abuja tarayyan Nigeriya. An yi wannan taro ne dakin taro na Merit House dake Abuja.Bayan bude taro da addu’a ne,Dr Shu’aibu ya bayyana maqasudin taron da taken taron da kuma mutanen da zasu gabatar da kasida a wajen taron. Hon.Ebenezer Oyintikin,daya daga cikin wa’yanda suka gabatar da kasida a wajen ya bayyana cewa shi kirista ne amma yana amfani da wani hadisi ya samu daga Annabi Muhammadu(sawa) cewa: “Idan abinda zaku saya ma ‘ya’yanku ba zasu isa ku raba ku hada da yaran makwabtanku ba,to,ku basu a cikin gida kar ku sake su fita dashi waje.” Ya cigaba da cewa ya san Harkar Musulunci wadda Sheikh Zakzaky yake jagoranta ta doru ne akan wannan hadisi na Annabi da tsari na tausayi ga al’umma da jin kai. Shi kuma Hon.Deji Adeyanju a nashi jawabin cewa yayi: “Ban taba ganin lalatacciyar gwamnati kamar ta Nigeriya ba.Basa girmama mutanen kirki masu ilimi amma suna sasanci da lallaban ‘yan ta’adda.Na tabbata da shi’a suna da makamai da tuni gwamnati ta fara sasanci da su. “Takurawar da gwamnati take maku ta kaikace tana fada maku ne ku dauki makamai ku zama ‘yan ta’adda,sai ku kuma kuka nuna masu kuna da hankali da tunani.” Deji ya nuna takaicinsa dangane da lalacewan kasan nan,yana cewa: “Ya gwamnati zata kashe mutum sama da 1000 amma shugaban kasa ya fito gidan talabijin yana cewa “me yasa suke dukan kirjin soja?”Wallahi baka da Kalmar da zaka iya fassara wannan gwamnati.” Dr John Danfulani a lokacin da yake gabatar da nashi bayanin ya bayyana abubuwan alkairi da ya gani game da Harkar Musulunci a Nigeriya,yana cewa: “Na halarci ayyukan da tarukan IMN da yawa fiye da yadda wani dan IMN din.Na je Tattakin Arba’een,na ga bayin Allah da aka kashe a lokacin tattakin,na ziyarci Sheikh Zakzaky lokaci daban daban.Na fahimci cewa ‘yan harka suna da tsari kuma suna tare da Allah.Ya za a yi cikin kasa da shekara 40 ya zama an iya samar da mutane sama da miliyan 20 in ba abin Allah ba? “Kaman yanda na ga wani hadisi yana cewa shi mutum imma dan uwanka ne a halitta ko dan uwanka a addini.Kuma shi’a sun yi riko da wannan hadisin ta yanda suke mu’amala da kowa kamar yadda ya gabata.Har yanzu ba zaka taba samun dan shi’a dan ta’adda ba,dukkan bangarorin ISIS,DAESH da Boko Haram dukkansu ba shi’a bane.” Daga cikin wa’yanda suka gabatar da kasida a wajen taron akwai;Professor Chidi Odunkalu,Alhaji Muktar Sirajo,da sauransu. Sheikh Abdulhamid Bello ne ya wakilci Sheikh Yakubu Yahaya Katsina a taron.Sannan da aka zo kaddamar da littafin da aka wallafa,sun sayi kofi biyu akan kudi naira dubu dari ga Sheikh Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah Ibrahim. Sannan Ahlul Dothour sun sayi kwafi 10 akan kudi naira dubu dari biyu,sai Malam Gamawa ya sayi kwafi 10 akan kudi naira dubu dari biyu da hamsin ga Shugaba Muhammadu Buhari da Gwamna Nasiru ElRufa’I da Sufeto Janar na ‘yan sanda da sauransu. Duk da ‘yan sanda sun kawo ziyara wajen sun tafi ba tare da wani abu ya faru ba,kuma an kammala taron lafiya cikin nasara.

  cigaba ...
 • Almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky sun yi muzahara a Abuja domin tunawa da shahidan Quds na 2014

  A yau laraba 26 ga watan Yuli 2017 ne daruruwan almajiran Sheikh Ibrahim Yakubu Zakzaky suka yi gaggarumar muzahara a birnin tarayya Abuja domin tunawa da 'yan uwansu da aka kashe a lokacin muzaharan Quds ta 2014. Sun fara muzaharan daga Area 2,suna tafiya cikin tsari da natsuwa suna dauke da hotunan Sheikh Zakzaky da banonin da aka rubuta free Zakzaky,Free Palastine.Suna rera waqoqi iri-iri wadanda suke alamta neman a yantar da Falasdinu,da kuma gwamnatin Nigeriya ta gaggauta sakin Sheikh Zakzaky da mai dakinsa ba tare da sharadi ba. Sun karkare muzaharan da kona tutan Isra'ila a park na Area 1,sannan suka yi addu'a kowa ya watse ba tare da wani abu ya faru ba kaman yanda majiyar mu ta shaida mana. In ba a manta ba a shekarar 2014 ne a lokacin da almajiran Sheikh Zakzaky suka fito Muzaharan Quds a Juma'ar karshen Ramadan din shekaran ne, sojoji suka zo suka bude wuta akan masu muzaharan wanda yayi sanadin shahadan sama da mutum 30 wanda ya hada 'ya'yan jagoran harkar musulunci a Nigeriya Sheikh Ibrahim Zakzaky.

  cigaba ...
 • Jami’an tsaro sun tarwatsa masu taron tunawa da Shahidan Quds 2014

  A yau ne da gamayyan jami’an tsaron da suka hada da Mopol da ‘yan sanda da sojoji suka zo farfajiyar filin Darur Rahma dake a kan hanyar zuwa Jos a lokacin da ake yin taro domin tunawa da ‘yan uwa almajiran Sheikh Zakzaky da sojoji suka kashe a Muzaharan Quds ta 2014 suka umurci kowa da kowa da ya watse a ya bar wajen. Jami’an tsaron da suka je Darur Rahma domin tarwatsa masu wannan taro sun kai kimanin mota 8 zuwa 10 dauke da muggan makamai suna umartan mahalarta taron da su bar wajen taron. Ganin haka ya sanya jagororin taron suka yi addu’a suka ziyarci shahidan dake kwance a wajen,sannan suka fito daga wajen cikin natsuwa,su kuma jami’an tsaron gefe guda suna bin su a baya har suka fito bakin titi suka hau ababen hawansu suka tafi suka bar wajen. A lokacin da majiyarmu ta tuntubi AC din Zariya,ACP Ibrahim akan ko me yasa jami’an tsaro suka je wajen wannan taro domin su hana shi?Sai yace : “akwai matsala ne a wajen shi yasa suka basu shawara su bar wajen.” Shi kuma Sheikh Abdulhamid Bello,daya daga cikin jagororin wannan taro cewa yayi: “Mun saba duk shekara muna shirya irin wannan taro domin tunawa da ‘yan uwanmu su 34,ciki har da ‘ya’yan jagoranmu guda uku da aka kashe a shekarar 2014. “Mun fara taron da karfe 8:00 na safe,can wajen karfe 10:00 na safe sai ga jami’an tsaro sun zo sun same mu,da farko sun fara zagaye mu ne ba tare da sun ce komai ba,sai muka cigaba da taron mu. “Zuwan ‘yan sanda karkashin jagorancin ACP ked a wahala,sai suka fara kawo mana cikas a taron,sun ta kokarin su sa mu harzuka amma ba suyi nasara ba.Sai suka zo suka cewa mai wa’azi ba damuwa,yi ka gama ka karkare ku tashi ku bar wajen.” Sheikh Bello ya sheda ma majiyarmu cewa taron ya samu halartan almajiran Sheikh Zakzaky daga garuruwan kusa da nisa kuma anyi jawabai masu yawa kafin zuwan jami’an tsaro su kawo cikas

  cigaba ...
 • An Gabatar Da Muzaharar Lumana A Abuja

  A jiya laraba ne, matasa karkashin dandamalin daliban harkar musulunci na Nigeriya suka gudanar da muzaharan lumana a garin Abuja, domin neman gwamnatin Nigeriya ta bi umurnin kotu ta saki jagoransu Sheikh Ibrahim Zakzaky wanda yake a tsare a hannun DSS tun Disambar 2015 duk da babban kotun tarayya tayi umurni da sake shi a watan Disambar 2016. In ba a manta ba sojoji a lokacin da suka kai wannan hari a gidan Sheikh Zakzaky dake Zariya sun harbi malamin a wurare da dama na jikinshi wanda yayi sanadin rasa idonsa daya.Sannan an kashe masa 'ya'ya uku tare da harbin mai dakinsa a qugu. Wadannan matasa dalibai sun gudanar da wannan muzaharan cikin tsari,suna dauke da kwalaye an rubuta free zakzaky, suna wake na neman a saki jagoransu,suna tafiya har zuwa inda zasu kulle muzaharan,kawai sa 'yan sanda suka zo suka fara antaya masu tiyagas. Har zuwa lokacin hada wannan labarin bamu da labarin kama wani daga cikin masu muzaharan ko samun rauni daga cikinsu. Kuna iya ganin wasu hotunan muzaharan a kasa:

  cigaba ...
 • Ana yunkurin hallaka Sheikh Zakzaky

  Shugaban dandalin yada labarai na harkar musulunci a Nigeriya,Ibrahim Musa ya fadi a wata takarda ta manema labarai da ya aiko da ita yau 19 ga watan 2017 cewa an yunkurin hallaka jagoran harkar musulunci a Nigeriya.Yana cewa:

  cigaba ...