• An yi gangamin a Saki Sheikh El-Zakzaky a birnin Oslo na kasar Norway

  Dimbin al'umma ne suka yi wani gangami a birnin Oslo na kasar Norway suna neman a saki jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky da gaggawa. Mahalarta wannan gangamin sun rika daga hotunan Sheikh El-Zakzaky suna rera taken lallai gwamnatin Nigeria ta yi.........

  cigaba ...
 • An yi gangamin "A saki Sheikh El-Zakzaky" a birnin Newyork na Amurka

  Dimbin al'umma ne suka yi wani gangami a birnin Newyork na kasar Amurka a yau lahadi suna Neman a saki jagoran Harkar Musulunci a Nigeria Sheikh Ibraheem Yaqoub El-Zakzaky da gaggawa. Mahalarta wannan gangamin sun rika daga hotunan Sheikh El-Zakzaky suna rera taken lallai gwamnatin Nigeria ta yi gaggawar sakin malam.288

  cigaba ...
 • Muzaharar a saki Zak zaky a Mashad

  A dazun nan ne dubun dubatan al'ummar musulmi suka gabatar da wata muzaharar Neman a saki Sheikh El-Zakzaky, wadda aka dauko ta daga haramin limami na takwas cikin jerin limaman shiriya na gidan Manzon Allah[SAWA] watau Imam Ridha[AS]. Mahalrta wannan muzahara sun rika daga hotunan Sheikh El-Zakzak.288

  cigaba ...
 • An gudanar da Arba’in Hussaini a Saudiyya

  Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s}-abna-an gudanar da juyayin Arba’in na Imam Hussain{a.s} a yankin Katif dake gabashin Saudiyya inda mafiyawan mazauna yankin ‘yan shi’a ne.288

  cigaba ...
 • Daliban Hauzar musulunci a Qum sun nuna goyon bayansu ga al’ummar Yemen

  Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti-abna-ayau ne dalibai da malaman Hauzar musulunci na garin Qum suka taru a makarantar Feziya domin nuna goyon bayan su ga al’ummar Yemen da kuma Allah wadai da harin fin karfi wanda kasar Saudiya ke kaiwa a kan Yemen. A wurin taron Ayatullah Ahmad Khatami na’ibin Limamin Juma’a na Tehran ne ya gabatar da jawabi ga mahalarta taron.ABNA

  cigaba ...
 • Karancin wutar Lantarki a Yemen

  Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s}-abna-sakamakon hare-haren jiragen yakin Saudiya da na hadin gwiwar wasu kasashe yayin sanadiyar rasa wutar Lantarki a wasu sassa na kasar Yemen musumman babban birnin wato San'a. Kasar Saudiya na cigaba da kai hari kan ma'aikatu da kasuwanni, wanda hakan ke shafar fararen hula.ABNA

  cigaba ...
 • Wasu 'yan Yazidi da 'yan ta'adda na Da'ish suka sako

  Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S}-abna-'yan ta'adda na kungiyar Da'ish sun sako sama da mutane 200 yan kabilar Yazidi da suka sace tsawon lokaci, a cikin wadanda akan 'yanto akwai yara sama da 40 da kuma tsofaffi da marasa lafiya.ABNA

  cigaba ...
 • Masallata a Tehran sunyi Allah wadai da harin Saudiya akan Yaman

  Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S}-abna-a yaune bayan idar da sallar Juma’a a Tehran babban birnin Iran aka gabatar da zanga-zanga domin nuna rashin amincewa da hare-hare fin karfi da kasar Saudiya tare da hadin gwiwar kawayenta ke kaiwa akan Yaman. Masallatan na dauke da kwalayen la’anta Amruka, Isra’ila da kuma iyalan sa’ud, suna kuma rera wakar goyan bayan su ga al’ummar kasar Yaman.ABNA

  cigaba ...
 • Rauhani; takunkumi ba zai yi tasiri ga Iran ba

  Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S}-abna-Hujjatul islam walmusilimin Hassan Rauhani yayin da yake Magana da al’ummar kasar ta gidan talabijin kai tsaye ya bayyana cewa, al’umma kasar Iran ta nunawa Duniya cewa takunkumi da takurawa ba zaiyi nasara wurin kawar da kasar a shirinta na makamashin Nukiliya ba. A cigaba da jawabin sa ya yabawa jagoran juyin musulunci na Iran Ayatullahi Sayyid Ali Khamna’I a bisa goyan bayan da ya ba wakilan kasar a yayin da suke tattaunawa da takwarorin aikin su na kasashen 5+1. Rauhani yace; aiyukan fasaha na makamashin Nukiliya hakkin Iran ne sannan kuma dole ne a cirema kasar duk wani takunkumi da aka kakafamata. A jiya ne kasar Iran da kasashen 5+1 suka rattafa hanun akan a mincewa da aiyukan makamashin Nukiliya na zaman lafiya na Iran.ABNA

  cigaba ...
 • Mutanen Takrit na komawa gidajen su

  Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti-abna-bayan ‘yanto garin Takrit daga hannun ‘yan ta’adda na kungiyar Da’ish, mutanen garin sun fara komawa gidajensu bayan tsawon lokaci suna gudun hijira. Garin Takrit na daya daga cikin garuruwan da sojin Iraki tare da hadin gwiwar sojin sa kai su kayi nasarar ‘yantowa daga kungiyar Da’ish.ABNA

  cigaba ...
 • Garin Takrit Iraki a cikin hotuna

  Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S}-abna-garin Takrit ya fada hannun sojojin Iraki tare da hadin gwiwar sojin sa kai, tsawon lokaci dai garin Takrit na cikin mamayar ‘yan ta’adda na kungiyar Da’ish.ABNA

  cigaba ...
 • Zaben Nigeria a cikin Hotuna

  Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S}-abna-a jiya Asabar ne a ka fara kada kuri’ar neman shugabancin Nigeria tsakanin Janar Muhammad Buhari da kuma shugaba mai ci yanzu wato Goodluck.ABNA

  cigaba ...
 • An gabatar da jana’izar Shahidai 142 a Yaman

  Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S}-abna-an gabatar da jana’izar Shahidai 142 a San’a babban birnin Yaman, inda dubban mutane suka halarta. In ba a manta ba a satin da ya gabatane wasu ‘yan kunar bakin wake na kungiyar Da’ish ne suka kai hare-hare a Masallatan Juma’a guda biyu wanda hakan yai sanadiya Shahadar mutane da dama ya kuma jikkata wasu.Abna

  cigaba ...
 • Tattakin maraja’a a Kum a ranar shahadar Fatima{S.A}

  Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S}-aba-Ayatullahi Wahid Khurasani, Ayatullahi Safi Ghulphaigani biyu daga cikin manyan maraja’a na shi’a ne suka fito yin tattaki da kuma juyayin shahadar Fadima{s.a} a garin Kum a yau talata. shi dai tattakin ya soma ne daga gidaje maraja’an zuwa Haramin Ma’asumma inda masu juyayin shahadar suka taru domin nuna bakin cikin su da abunda a kai ma iyalin Manzon Allah{s.a.w.w}.ABNA

  cigaba ...
 • Wata sojan Syria a fagen daga

  Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{A.S}-abna-ana horar da mata aikin soja a Syria bayan sun kare horon sais u gwamu da sauran soji domin yaki da kungiyoyin ‘yan ta’adda da suka addabi al’ummar kasar ta Syria.ABNA

  cigaba ...
 • Shahadar daya daga cikin manyan Ansarullah

  Kamfanin dillancin labarai na Ahlulbaiti{A.S}-abna-duban mutane suka fito a birnin San'a na kasar Yaman domin yin Allah wadai da kashe daya daga cikin manyan jagororin Ansarullah kuma wakilin kungiyar a majalisar tattaunawa ta kasa. Abdulkarim Alkhiwani yayi shahada ne sakamakon harin da wasu 'yan bindiga suka kai masa a San'a babban birnin Yaman.ABNA

  cigaba ...
Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni