• 'Yan Shi'a Mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky Sunyi Muzaharan Neman A Saki Jagoransu

  A jiya Alhamis 12 ga watan Oktoba,'yan shia mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky sun yi muzahara ta lumana domin jaddada kira ga gwamnatin Nijeriya da gaggauta sakin jagoransu wanda ya kwashe fiye da watanni ishirin yana tsare tun bayan harin ta'addancin da rundunar sojan Nijeriya ta kaddamar akan shehin malamin da mabiyansa a watan disambar 2015. Anyi wannan muzahara cikin tsari da nizami ana wakokin kira da gwamnati ta mutunta hukuncin kotu ta saki malamin ba tare da wani sharadi ba. Duk da halartan jami'an tsaro a wajen muzaharan babu wani abu da ya faru mara dadi

  cigaba ...
 • ASHURA 1439 RANA 7

  Wasu hotunan zaman makokin shahadar Imam Husain (as) a Karbala wanda mabiya babban malamin Shi'a a Nijeriya wato Sheikh Ibrahim Zakzaky suka gabatar yau a garuruwan da suka hada da Katsina,Kano,Gombe,Sokoto,Saminaka da sauran wurare. Duk da jami'an tsaro sun so su kawo ma zaman cikas a Sokoto amma dai an yi kuma an tashi lafiya

  cigaba ...
 • ASHURA 1439 RANA TA 6

  ASHURA 1439 RANA TA 6 Wasu hotunan zaman makokin tunawa da shahadar Imam Abu Abdillahil Husain (as) wanda 'yan shi'a mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky suka gabatar a garuruwan Kaduna,Katsina,Kano,Potuskum da sauransu.

  cigaba ...
 • ASHURA 1439 RANA TA 6

  ASHURA 1439 RANA TA 6 Wasu hotunan zaman makokin tunawa da shahadar Abu Abdillahil Husain (as) a cibiya da rassan kungiyar Rasulul A'azam wanda Sheikh Muhammad Nur Das yake jagoranta.

  cigaba ...
 • ASHURA 1439 RANA TA 5

  Kuna iya ganin hotunan zaman makokin Shahadar Imam Abu Abdillahil Husain wanda 'yan Uwa almajiran Sheikh Ibrahim Yakubu Zakzaky suka gabatar yau a garuruwan da suka hada da Kaduna,Kano,Nassara,Malumfashi,Uduwa da sauransu

  cigaba ...
 • ASHURA 1439 RANA TA 3

  A jiya ma kaman sauran kwanaki 'yan shia mabiya Sheikh Ibrahim Zakzaky sun gudanar da zaman makoki domin tunawa da Shahadar Imam Husain a Karbala. Daga cikin garuruwan da aka yi wannan zama akwai Kaduna,Katsina,Kano,Zariya,Sokoto,Yola,Potuskum da sauransu. Kuna iya ganin wasu hotunan zaman a kasa:

  cigaba ...
 • LABARI CIKIN HOTUNA:

  Mu'assasar Thaqafar Thaqalayn Kaduna tana gudanar da taron Eidin Ghadeer a dakin taro na gidan Arewa dake Kaduna. Sheikh Hamzah Muhammad Lawal ne yake gabatar da hujjoji da bayanai masu yawa domin tabbatar kasantuwar Imam Ali a matsayin kalifan Manzon Allah(sawa).

  cigaba ...
 • Rana Ta Uku:Bukin Tunawa Da Munasabar Haihuwan Imam Ali Ibn Musa Ar-Ridha a Kano

  Yau Asabar,5 ga watan Agusta 2017,ta zama ranar khatma na taron tunawa da munasabar haihuwan Imam Ali Ibn Musa Ar-Ridha da kuma sanya tuta a Hussainiyyar Kofar Waika Kano. In ba a manta ba,wannan taro na Ad-Da’iral Ammah ce wanda Sheikh Zakzaky ya umurci Sheikh Sanusi AbdulKadir da ya shirya shi a garin Kano a wannan shekaran.Yau ce rana ta uku kuma ta karshe daga cikin kwanaki uku da aka dauka ana yin taron a Markaz dake Kofar Waika Kano tarayyar Nigeriya. Bayan bude taro da addu’a da wakokin bege daga sha’irai,malamai da dama sun yi jawabai masu yawa dangane da munasabar da aka taro domin ta. Sarkin Sharifan Kano a nashi jawabin ya bayyana cewa: “Duk wanda kuka ga ya shirya taron hadin kan musulmi amma bai gayyaci ‘yan shi’a ba,munafuki ne.Ba taron hadin kai bane,taron ya za a far wa ‘yan shi’a ne da neman biyan bukatunsu kawai.Ni Bakadire ne,kuma dan darika,na yarda ‘yan shi’a musulmai ne,kuma zan yi taro da su. “Gidanmu ya kai shekara dari shida da sharifanci amma ban taba ganin tutar kabarin wani Imami ba,sai a gun ‘yan shi’a.” Sarkin Sharifan Kano ya yi kira da roko ga Sheikh Sanusi AbdulKadir cewa ‘don Allah a taimaka a shiga da wannan tuta ta Imam Ridha cikin Sharifai a zagaya mana da ita a nuna masu cewa gashi wajen ‘yan shi’a.’ Sarkin Sharifai bai karkare jawabinsa ba sai da yayi kira ga hukuma yana cewa: “Wannan taruka da ake yi na Imam Ridha sune suke zaunar da kasar nan lafiya.” Shi kuwa Sheikh Yakubu Yahaya Katsina a lokacin da yake gabatar da jawabinsa a matsayin babban bako a wajen taron, yayi bayani ne game da muhimmancin riko da Imam Ali a matsayin wanda yake massala sunnar Annabi Muhummad(sawa),yana cewa: “A lokacin da aka kawo Imam Ali wajen zaben khalifa na uku an bashi zabi akan in zai yi aiki da sunnar Annabi da sunnar khalifofi guda biyu,sai Imam Ali yace;zan yi aiki da Manzon Allah.Don haka idan kana neman sunnah,to,Imam Ali shine sunnah.” Sheikh Yakubu Yahaya ya bayyana cewa ‘Sheikh Zakzaky ya riga yayi jihadi kuma ya riga ya kafu.Ya ‘yantar da zukata,sun yi bara’a kuma sun yi wilaya,an canja tunaninsu.’ Sheikh Sanusi Abdulkadir a lokacin da yake jawabinsa a matsayin mai masaukin baki,ya bayyana cewa: “Don girman Allah don matsayin Imam Ali Ar-Ridha don albarkan wannan tuta idan da wanda muka yi wa laifi,don girman wannan rana tuta ya yafe mana. “Mu idan da wanda yayi mana laifi Wallahi mun yafe masa.Ranar sa wannan tuta ta zama ranar hadin kanmu.” Taron ya samu halartan ‘yan uwa daga sassa daban daban a cikin Nigeriya a kasashen makwabta.Daga cikin wadanda suka halarci wannan taro akwai Sheikh Adamu Tsoho Jos,Sheikh Kasimu Umar Sokoto,da Malam Abubakar Nuhu Talatan Mafara da sauran manya manya wakilan ‘yan uwa almajiran Sheikh Zakzaky daga garuruwa masu yawa

  cigaba ...
 • TAWAQAR ‘YAN UWA ALMAJIRAN SHEIKH IBRAHIM ZAKZAKY SUN ZIYARCI SHEIKH ABDULJABBAR SHEIKH NASIRU KABARA Da SHEHU USMAN DAHIRU BAUC

  Jiya talata,19 ga watan Yuni 2017 ne,wata tawaqa ta almajiran Sheikh Ibrahim Yakubu Zakzaky karkashin jagorancin Sheikh Yakubu Yahaya Katsina suka ziyarci Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabari a mahallin da shehin malamin yake gabatar da karatun tafsirin Alkur’anin na “Jauful Fara”. Shaikh Abduljabbar Nasiru Kabara malami ne masani wanda a lokaci guda kuma marubuci na kin karawa.Ya rubuta littafai masu yawa a janibobi daban daban.Sannan saboda tsabagen kauna da soyayya da shehin malamin yake nuna wa Manzon Allah da iyalan gidansa tsarkaka,ya sanya mutane daga bangaren Salafiyya suna jifan malamin Tashayyu’I. Sheikh AbdulJabbar ya amshi wannan tawaqa cikin girmamawa da farin ciki,sannan tawaqar ta nuna farin ciki dangane da irin tarbar da Sheikh yayi masu. A cigaba da ziyara ta jiya,tawaqar ‘yan uwa almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky karkashin jagorancin Sheikh Yakubu Yahaya Katsina suka ziyarci Sheikh Dahiru Usman Bauchi domin girmama da sada zumunci. Sheikh Dahiru Bauchi babban malamin addinin musulunci ne kuma yana daga cikin manya manyan muqaddiman Tijjaniyya a Nigeriya.Malami ne mahardacin kuma masanin tafsirin Alkur’ani da littafai,yana daga cikin wa’yanda karatukansu da maganarsu ke daukan hankalin jama’a a NIgeriya saboda hikima da iya bayani,ma’ana yana da tasiri matuka a cikin al’umman Nigeriya. Sheikh Yakubu Yahaya Katsina yayi taqaitaccen bayani game da dalilin wannan ziyara tasu,daga cikin abubuwan da ya fadi akwai cewa: “Dan shi’an dake zagin Sahabbai kaman dan haqiqa ne a cikin tijjaniyya ko dan izala a cikin Ahlus-Sunnah”. A lokacin da Shehu Dahiru Bauchi yake jawabin maraba ga wannan tawaqa ya shaida cewa: “Duk musulmi shi’ar Annabi Muhammadu ne,idan musulmi yace baya shi’a sai mu kore shi.Mun sha yin wazifa tare da Sheikh Zakzaky,sannan gashi kun yi sallah a bayana na kuma kun yi salatul Fatihi. “Maganar zagin Sahabbai kuwa tattaunawa da masu hankali cikinku yasa mun fahimci ‘yan haqiqan dake cikinku sune suke yi.Don haka mun yarda da abubuwanku dari bisa dari kaman yadda kuka yarda da na mu. Wannan tawaqa ta Sheikh Yakubu Yahaya tayi sallah tare da Shaikh Dahiru,sannan suka yi buda baki tare da shi a masaukinsa dake Kano.

  cigaba ...
 • DALIBAI SUN YI KIRA DA A SAKI SHEIKH IBRAHIM ZAKZAKY A GARIN ABUJA NIGERIYA

  A jiya laraba ne,daliban manyan makarantu na harkar musulunci suka gudanar da muzaharar lumana a garin Abuja domin kira da gwamnatin Nigeriya da ta bi umurnin kotu ta sakin Sheikh Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenat wa’yanda suka kasance a tsare tun bayan lokacin da sojojin Nigeriya suka afka ma Sheikh da almajiransa a watan Disambar 2015. Shugaban kungiyar ta daliban,S I Ahmad a wata takarda da suka rabawa manema labarai wadda suka yi ma take da “Lokaci yayi da gwamnatin Nigeriya zata saki Sheikh Zakzaky” ya bayyana cewa: “Mai yasa hukumomin Nigeriya suka ki su bi umurnin babban kotu,su saki Jagoran harkan musulunci a Nigeriya,Sheikh Zakazaky tare da mai dakinsa wa’yanda suke tsare ba akan ka’ida ba? “Yanzu ta bayyana ma duniya cewa Sheikh Zakzaky da mai dakinsa Malama Zeenah,suna tsare fiye da shekara daya da rabi ba tare da wata tuhuma ko laifi ba tun bayan farmakin rashin imani da sojojin Nigeriya suka kai ma malamin da almajiransa wanda yayi sanadiyyan asaran rayukan daruruwan almajiransa maza da mata da kananan yara a Zariya.Sojojin Nigeriya sun afka ma Sheikh Zakzaky da matansa a gidansa.Sun harbi malamin a wajaje masu yawa a jikinsa tare matansa,suka kashe masa ‘ya’ya a gabansa. Daliban masu muzaharan lumana din sun kasance cikin tsari sanye da riguna iri wa’yanda aka rubuta a saki Zakzaky da huluna,suna rike da banoni wa’yanda aka rubuta a saki Zakzaky da kuma gwamnati tabi umurnin kotu,suna wakoki na kira da a saki Zakzaky.An kammala muzaharan lafiya ba tare da wani matsala ba

  cigaba ...
 • "Acadamic Forum" sun gabatar da gangami a gaban majalisar dokoki ta kasa

  A jiya Laraba 10 ga watan Mayu 2017 ne 'yan uwa dalibai na "Acadamic Forum" suka shirya wani gangami na tunatarwa a gaban ginin majalisar dokoki ta kasa a Abuja babban birnin tarayyar Nigeria. Gangamin dai wanda ya sami halartar dimbin al'ummar musulmi an gabatar da shi ne da nufin sake tunawa 'yan majalisa

  cigaba ...
Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni