Iran Ta Maida Martani Kan Zargin Cewa Tana Tsoma Baki A Harkokin Kasashen Larabawa

  • Lambar Labari†: 809546
  • Taska : Pars Today
Brief

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran ya bayyana zargin baya-bayan nan da kasar Hadaddiyar Daular Larabawa ta yi kan Jamhuriyar Musulunci ta Iran da cewa: Zargi ne maras tushe ko makama.

A taron manema labarai da ya gudanar a jiya Asabar: Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Iran Bahroum Qasimi ya bayyana cewa: Zargin da minista mai bada shawara kan harkokin siyasar wajen kasar Hadaddiyar Daular Larabawa Anwar Qarqash ya yi kan kasar Iran cewa; Tana tsoma baki a harkokin da suka shafi kasashen Larabawa, zargi ne maras tushe, kuma a maimakon haka kamata yayi ya zurfafa tunani kan hanyoyin karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu tare da girmama kasashen da suke makobtaka da juna.

Bahroun Qasimi ya kara da cewa: A maimakon kokarin kara zafafa matakin sabani a tsakanin kasashen yankin tekun Pasha, kamata ya yi ya kirkiro hanyar gudanar da zaman tattaunawa da nufin warware duk wata takaddama ko rashin fahimtar juna a tsakanin kasashen da suke da makobta, saboda Jamhuriyar Musulunci ta Iran a kullum kokarinta shi ne ganin an samu zaman lafiya da sulhu a dukkanin yankin.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky