Zarif: Hana Musulmi Shiga Kasar Amurka Karfafa Masu Tsaurin Ra'ayi Ne

  • Lambar Labari†: 808068
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya mai da martani kan matakin da shugaban kasar Amurka ya dauka na rattaba hannu kan dokar hana al'ummar Musulmi shiga cikin kasar ta Amurka.

A martaninsa ga matakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya dauka na rattaba hannu kan dokar hana takardar izinin shiga cikin kasar Amurka ga duk wani musulmi wato Visa; Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad Jawad Zarif a shafinsa na Twitter ya bayyana matakin da cewa wata babbar kyauta ce ta Amurka ga masu tsaurin ra'ayi da akidar wuce gona da iri a tsawon tarihin duniya.

Har ila yau Muhammad Zarif ya bayyana cewa: Kafar dokar a kan hana al'ummun wasu kasashe bakwai na musulmi lamari ne da ke fayyace rashin muhimmancin da'awar mahukuntan na Amurka. 288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky