Iran Ta Yi Allah Wadai Da Gine-Ginen Matsugunan Yahudawan Sahayoniyya A Yankunan Palasdinawa

  • Lambar Labari†: 807374
  • Taska : Pars Today
Brief

Kakakin ma'aikatar harkokin wajn kasar Iran ya yi tofin Allah tsine kan yadda gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila take ci gaba da mamaye yankunan Palasdinawa ta hanyar gudanar da gine-ginen matsugunan yahudawan sahayoniyya.

Bahran Qasimi ya kara da cewa: Matakin da gwamnatin haramtaciyar kasar Isra'ila ke dauka na ci gaba da mamaye yankunan Palasdinawa ta hanyar gudanar da gine-ginen matsugunan Yahudawan Sahayoniyya lamari ne da ya yi hannun riga da dokokin kasa da kasa, don haka abin yin Allah wadai ne, kuma dole ne kungiyoyin kasa da kasa da gwamnatocin kasashen duniya su dauki matakan sanya matsin lamba kan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra'ila.

A ranakun bukukuwan rantsar da sabon shugaban kasar Amurka Donald Trump mahukuntan gwamnatin haramtaciyar kasar Isra'ila suka kada kuri'ar amincewa da gudanar da sabbin gine-ginen matsugunan yahudawan sahayoniyya 'yan kaka gida 2500 a yankunan Palasdinawa da suke gabar yammacin kogin Jordan. 288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky