Iran Ta Nuna Rashin jin Dadi Dangane Da Abin da Ke Faruwa A najeriya

  • Lambar Labari†: 724815
  • Taska : Hausa.ir
Brief

Ma'aikatar harkkokin wajen kasar Iran ta nuna damuwa dangane da abin da yake faruwa a Najeriya na kai hare-hare kan masu gudanar da tarukan addini a Zariya.

Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran Hussain Jabir Ansari ne ya bayyana hakan a jiya, yana mai ishara da abin da ya faru na kai hari da sojojin Najeriya suka yi kan gidan Sheikh Ibrahim Zakzaky jagoran harkar muslunci.

Ya ci gaba da cewa ko shakka babu a halin yanzu Najeriya na bukatar zaman lafiya da kwanciyar hankali, ta yadda ya kamata a warware matsaloli irin wannan ta hanyar tattaunawa da fahimtar juna, tare da mayar da hankali ga babbar matsalar da kasar take fuskanta ta rashin tsaro da batun ta'addan, wanda shi ne bababn abin da ke ci ma kasar tuwo a kwarya.288


Labarun da suka dace

Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky