Rasha Da Iran Sun Jaddada Wajabcin Yin Aiki Tare Domin Habbaka Tattalin Arzikinsu

  • Lambar Labari†: 653896
  • Taska : hausa.irib.ir
Brief

Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya sheda wa shugaban kasar Iran Sheikh Hassan Rauhani cewa Rasha za ta yi iyakacin kokarinta domin ganin an kawo karshen takaddamar da ake yi kan shirin Iran an makamashin nukiliya, ta hanyar cimma yarjejeniya ta karshe tare da manyan kasashen duniya.

Shugaba Putin ya sheda wa shugaba Rauhani hakan a wata zantawa da ta hada ta wayar taro a daren jiya, inda shugaban na Rasha ya ce za su ci gaba da yin aiki tare da Iran a dukkanin bangarori, domin kara habbaka tattalin arzikinsu, inda ya  ce janye warware takaddama kan shirin Iran na makamashin nukiliya zai taikama wa dukkanin bangarorin Iran da Rasha a cikin mu'amalolinsu na cinikayya da tattalin arziki.

 

A jiya ne aka kammala zaman tattaunawa tsakanin Iran da manyan kasashen duniya a birnin Vienna na kasar Austria ba tare da cimma yarjejeniya ta karshe ba, amma dukkanin bangarorin sun amince da a ci gaba da tattaunawar domin kai wag a matsaya ta karshe. ABNA


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Jagora Ga Maniyyata Hajjin Bana (1438-2018)
We are All Zakzaky