Miliyoyin Al'ummar Iran Ne Suka Gudanar Da Bukukuwan Shekaru 38 Da Nasarar Juyin Musulunci Na Kasar

  • Lambar Labari†: 810739
  • Taska : Pars Today
Brief

Rahotanni daga bangarori daban-daban na kasar Iran na nuni da cewa miliyoyin al'ummar kasar ne suka fitowa kan titunan kasar don gudanar da jerin gwanon tunawa da shekaru 38 da samun nasarar juyin juha halin Musulunci a kasar.

A birnin Tehran, babban birnin kasar inda ake gudanar da mafi girman bikin, miliyoyin al'ummar kasar ne suka  gudanar da jerin gwanon daga bangarori daban-daban na birnin zuwa dandalin Azadi Square da ke kusan tsakiyar birnin inda suka sauraren jawabin da shugaban kasar Dakta Hasan Ruhani  ya gabatar  bayan an kammala jerin gwanon.

Bukukuwan na bana dai na zuwa ne a daidai lokacin da sabuwar gwamnatin Amurka ta Donald Trump ta sake sabunta irin barazana da kiyayyar shekaru aru-aru da gwamnatocin Amurka suke nuna wa al'ummar Iran da juyin juya halin Musulunci na kasar inda ta sake sanya wasu sabbin takunkumi wa kasar da kuma ci gaba da barazanar amfani da karfin soji a kan Iran din.

A ranar Litinin din da ta gabata dai Jagoran juyin juya halin Musulunci na kasar Iran din Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya bayyana cewar al'ummar Iran din za su mayar wa shugaba Trump din da martani a wannan ranar ta hanyar irin gagarumar fitowar da za su yi don nuna doyon bayansu ga tsarin Musulunci na kasar.

A ranar 22 ga watan Bahman (11 ga Fabrairun 1979) ne dai juyin juya halin Musulunci na kasar Iran karkashin jagorancin marigayi Imam Khumaini (r.a) yayi nasara inda a kowace shekara idan ranar ta zagayo miliyoyin al'ummar Iran din sukan fito don nuna goyon bayansu ga tsarin Musuluncin da kuma yin Allah wadai da ma'abota girman kai karkashin jagorancin Amurka.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky