Iran Ta Yi Watsi Da Sabon Takunkumin Amurka

  • Lambar Labari†: 809349
  • Taska : Pars Today
Brief

amhuriyar Musulunci ta Iran ta yi Allah wadai da sabon takunkumin da Amurka ta sanya mata saboda shirin makamai masu linzaminta na kariya tana mai cewa za ta mayar wa kura da aniyarta.

A cikin wata sanarwa da Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ta fitar a jiya Juma'a ta bayyana cewar: Jamhuriyar Musulunci ta Iran za ta mayar da martanin da ya dace ga duk wani kokari na cutar da manufar kasa da al'ummar Iran.

Sanarwar ta kara da cewa shirin makamai masu linzamin na Iran, wani shiri ne kawai na kariyar kai daga barazanar makiya kana kuma wani hakki ne da al'ummar Iran suke da shi karkashin dokoki na kasa da kasa da babu wani da ya isa ya hana su wannan hakki da suke da shi.

A jiya Juma'a ce dai gwamnatin Donald Trump ta Amurkan ta sanar da cewa ta kakaba wa Iran wasu sabbin jerin takunkumi, da suka shafi kamfanonin 12 da kuma wasu mutane 13 'yan kasar Iran da 'yan wasu kasashe na daban saboda gwajin makami mai linzamin da ta yi a kwanakin baya gwajin da Iran din da ma wasu kasashen duniya suka ce bai saba wa yarjejeniyar nukiliya da aka cimma da ita ba.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky