Jagora Ya Ziyarci Hubbaren Imam Khumaini (RA) Farkon Ranakun tunawa da juyin musulunci

  • Lambar Labari†: 808768
  • Taska : Pars Today
Brief

Jagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i ya ziyarci hubbaren marigayi Imam Khumaini (RA) da wasu daga cikin shahidan juyin Islama, a daidai lokacin da ake fara bukukuwan zagayowar ranakun fajr na juyin Islama a kasar.

Ayatullah Sayyid Ali Khamna'i a yayin ziyarar tasa, ya ziyarci kabarukan wasu daga cikin wadanda suka bayar da gudunmawa wajen kafa jamhuriyar muslunci,inda ya fara da kabarin Ayatullah Hashemi Rafsanjani, wanda ya rasu 'yan makonnin da suka gabata.

Bayan na kuma ya ziyarci kabrukan Shahid Beheshti, tsohon alkalin alkalan kasar da kuma Rajae tsohon shugaban kasar gami da Bahonar tsohon firayi ministan kasar, wadanda dukkaninsu suka suka yi shahada wajen bayar da gudunmawa ga juyin Islama.

Haka nan kuma jagoran ya ziyarci kabrukan wasu daga cikin wadanda suka yi shahada a wurin akre wurare masu tsarki na musulmi, da kuma wadanda suka rasa rayukansu daga cikin 'yan kwana-kwana a cikin makon da ya gabata, a lokacin kashe gobara a ginin Palsco a birnin Tehran.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky