Sakon Jagoran Juyin Musulunci Ga Kungiyoyin Dalibai Musulmi Na Kasashen Turai

  • Lambar Labari†: 806311
  • Taska : Pars Today
Brief

Wajibi ga dukkanin musulmi su shiga cikin fagen yaki da masu girman kai su ke yi da musulmi.

Jagoran juyin musulunci na Iran, Aatullah Sayyid Ali Khamnei ya ce: Wajibi ga dukkanin musulmi su shiga cikin fagen dagar yakin da masu girman kai su ke yi da musulmi.

Sakon da jagoran juyin musuluncin ya fitar a jiya juma'a ya kunshi cewa; Abinda ake jira daga gare ku, shi ne gina kawukansu a fagagen ilimi da addini da kyawawan halaye, sannan kuma yin tasiri a cikin muhallinku, ku kuma zama kari a cikin masu tafiya a tafarkin Allah da zance da kuma aikinku.

Ayatullah Sayyid Ali Khamnei ya kuma yi ishara da cewa samartaka da kuma zama dalibi suna a matsayin zango mai cike da kumaji da ya ke taimakawa ga manufa, kuma baya ga wannan ku dalibai kuna cikin kungiyar dalibai musulmi.

Gamayyar tarayyar turai ta taka rawa wajen wayar da kan al'ummar nahiyar a yunkurin juyin juya halin musulunci na Iran da kuma yunurin musulmi bakidaya.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

Sakon Shahadar Kwamandojin Musukunci. Haj,Kasim Sulemani Da Abu Mahdi
We are All Zakzaky
Tir Da Yarjejeniyar Karni