Zaman Ta'aziyyar Ayatullah Rafsanjani A Hussainiyar Imam Khumaini{R.A}

  • Lambar Labari†: 804296
  • Taska : pars today
Brief

An yi zaman ta'aziyyar Ayatullah Hashimi Rafsanjani a Husainiyyar Imam Khumaini (R.A) tare da halartar jagoran juyin juya halin muslunci Ayatullah Sayyid Ali Khamenei.

An yi zaman ta'aziyar, dangin marigayin tare da manyan jami'an gwamnatin Iran da suka hada da shugaban kasa da kuma shugaban majalisar dokoki gami da babban alkalin alkalai, gami da sauran dubban mutane daga ko'ina da suke halartar wurin.

A farkon zaman dai an bude wurin da karatun kur'ani mai tsarki, da kuma karato wasu daga cikin bayanai na manzon Allah (SAW) da iyalan gidansa tsarkaka.

A jiya ne dai aka gudanar da janazar Ayatullah Hashimi rafsanjani, wanda jagoran juyin juya halin muslunci Ayatullah Sayyid Ali Khamunai ya jagoranta, an kuma bizne gawar tasa ne a cikin hubbaren marigayi Imam Khumaini (R.A) da ke kudancin birnin Tehran.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky