Shugaban Kasar Iran Ya Taya Sabon Shugaban Ghana Nana Akufo Addo Murna

  • Lambar Labari†: 803561
  • Taska : Pars Today
Brief

Sabon shugaban Kasar ya yi alkawalin fada da talauci.

Kamfanin Dillancin Labarun Faransa ya ambato sabon shugaban kasar ta Ghana Nana Akufo Addo ya ce gwamnatinsa za ta maida hankali wajen karfafa kasuwancin daidaikun mutane a kasar, sannan ya kara da cewa: Babu wani dalili da zai sa ce talauci ya ci gaba da wanzuwa a cikin kasar.

Sabon shugaban kasar ta Ghana ya kuma ce wajibi a kara ma'aunin jin dadin al'ummar ta kasa, domnin baitul malin  kasar na yan kasa ne ba na wata jam'iyya ba.

Shugabannin kasashen Afirka da dama ne su ka halarci taron rantsar da sabon shugaban kasar ta Ghana wanda aka yi dazu da safe.

A gefe daya, shugaban kasar Iran Dr. Hassan Rauhani ya aike da sakon taya murya ga sabon shugaba na Ghana, NAna Akufo Addo, sannan kuma ya yi fatan ganin cewa alaka a tsakanin kasashen biyu ta ci gaba da bunkasa.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky