Wani Tsohon Sojan Amurka Ya Kai Hari a Tashar Jirgin Sama A Florida Ya Kashe Mutane 5.

  • Lambar Labari†: 803366
  • Taska : VOA
Brief

Harin ya kumma jikkata mutane takwas, ya janyo tsaiko a tashar na lokaci mai tsawo.

Hukumar binciken manyan laifuffuka ta Amurka FBI tace bata kawar da ta'addanci a zaman dalilin mummunar harin da aka kai a tashar jirgin sama dake birnin Fort Lauderdale dake jahar Flroida jiya Jumma'a ba. Jami'in hukumar George Piro, ya fada a wani taro da manema labari cikin dare dazu kenan anan Amurka cewa "hukumar tana binciken duk wata kafa" ciki harda ta'addanci.

Jami'an tsaro wadannda suke tsare da wanda ake tuhuman, sun ce sunansa Esteban Santiago,dan shekaru 26 da haifuwa, wanda ya sauka a tashar daga Alaska jiya jumma'a.

An hakikance ya bude wuta ya kashe mutane biyar, ya jikkata wasu takwas kamin a kama shi. Jami'in na FBI yace maharin yana dauke da bindiga ta hanu mai kwariya-kwariyar sarrafa kanta ta hanu.

An gano cewa, maharin tsohon soja ne a rundunar tsaron kasa da ake kira National Guard, a sansaninta dake Puerto Rico. A bara, a kashin kansa ya je a asibiti, ya nemi auna hankalisa, bayan da yace yana jin ana gaya masa ko bashi shawarwari ciki harda ya shiga kungiyar ISIS.

Santiago sojan Amurka ne a Iraqi na tsawon watanni 10 daga 2010-2011. Daga bisani ya shiga rundunar tsaron kasa dake Alaska jahar da tafi kowacce girma a Amurka, kuma wacce take da nesa can kuriya. Yayi aiki a rundunar daga shekara ta 2014 zuwa watan Agusta bara.288


Ka aiko da Ra'ayinka

Your email address will not be published. Required fields are marked *

*

پیام رهبر انقلاب به مسلمانان جهان به مناسبت حج 1440 / 2019
We are All Zakzaky